Sarkin Karaye Alhaji Dakta Ibrahim Ababakar II ya jinjinawa kokarin mataimakin shugaban Jami’ar kimiyya da Fasaha ta Wudil bisa Samar ingantattun tsare tsare a Jami’ar. Sarkin ya jadadda cewa, kirkirar sabbin kwasakwasai takwas a Jami’ar wanda mataimakin shugaban Jami’ar ya samar, hakan zai kara saukaka ilimi ga masu karamin karfi.
Sarkin ya bayyana haka ne alokacin da mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Alhaji yaje ta’aziyyar rasuwar tsohon kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Abdullahi Abubakar Karaye da Makaman Karaye Alhaji Musa Saleh Kwankwaso wadanda suka rasu kwanan nan.
Alhaji Dakta Ibrahim Ababakar II ya kuma kara jinjinawa mataimakin Jami’ar bisa Ta’aziyyar da ya kawo Fadar Ndoji da al’ummar Masarautar bisa rasuwar Makaman Karaye Alhaji Musa Saleh Kwankwaso wanda Sarkin ya bayyana a matsayin Uba da kuma tsohon kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano.
Tunda farko da yake gabatar da jawabinsa mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Shehu Alhaji cewa ya yi, shi da ‘yan Hukumar gudanarwar jami’ar sun girgiza matuka da samun labarin rasuwar wadannan fitattun mutane biyu.
Mataimakin shugaban Jami’ar ya yabawa Sarkin na Karaye Alhaji Dakta Ibrahim Ababakar II bisa kyakkyawan Jagoranci da kuma jajircewa wajen cigaban Masarautar. Ya kara da cewa, Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil zata ci gaba da hada karfi domin tabbatar da dorewar cigaban masarautar Karaye da ma sauran masarautun Jihar Kano.
Ya kuma yi amfani da wannan dama domin bayyanawa sarkin irin cigaban da jami’ar ta cimma, a shekarar data gabata an samar da sabbin kwasakwasai takwas a fannoni daban daban, ya yinda ake fatan samar da karin wasu a wannan ahekara. Kamar yadda jami’in yada labaran masarautar ta Karaye Haruna Gunduwawa ya shaidawa LEADERSHIP A A YAU.