Abdullahi Muhammad Sheka" />

Sarkin Karaye Zai Nada Kanin Kwankwaso Sarautar Makama

Sarkin Karaye

Masarautar karaye ta tsayar da ranar Juma’a 29 ga watan Janairun Shekara ta 2021 a Matsayin ranar da za’a nada kanin tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a Matsayin sabon Makaman karaye, Hakimin Madobi.

Alhaji Baba Saleh Musa Kwankwaso dan Majalisar sarkin karaye, guda cikin masu nada Sarakunan Masarautar ta karaye wanda za’a nada tare da sauran wasu mutane biyar.
Wadanda za a nada din sun hada da Alhaji Ibrahim Sani Gaya a Matsayin Sarkin Shanun karaye, Hakimin Shanono, Alhaji Abba Muhammad a Matsayin Ma’ajin Watarin karaye, Hakimin Kabo, Alhaji Bashir Maikudi Aminu a Matsayin San Turakin karaye da Kuma Alhaji Sadi Mustapha karaye a Matsayin dan masanin karaye, ya yinda Alhaji Ahmad Muhammad Tudun kaya za’a nada shi amatsayin Shettiman karaye.
Za a gudanar da bikin nadin a fadar Sarkin karaye wanda ake sa ran halartar Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da sauran manyan baki. Za Kuma a gudanar da bikin cikin tsauraran matakan kariya daga yaduwar annobar Korona.
Saboda haka masarautar ta karaye ke umartar dukkan wadanda za’a nada din sun tabbatar da Shaidawa wadanda suka gayyata wajen sanya takunkumin rufe hanci ya yinda aka tsara samar da sauran kayan kariyar kafin shiga wurin taron. Kamar yadda jami’in yada labaran masarautar ta karaye Haruna Gunduduwa ya shaidawa LEADERSHIP Ayau.

Exit mobile version