Sarkin Katsina Bukaci Iyaye Su Sa ‘Yaransu Makaranta

Sarkin KatsinaThe Emir of Katsina, Alhaji Abdulmumumi Kabir ya ba Iyaye shawarar su ‘ya’yansu makarantun Islamiyya da kuma na Boko .
Alhaji Kabir ya bada wannan shawarar ce a Katsina ranar Talata lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.
“ Ya ci gaba da bayanin cewar su aikin Iyaye ne su sa ‘ya’yansu makaranta, wannan kuma duk makarantun Islamiyya da kuma na Boko saboda samun ingantaccen ilimi.
“ Ita dai masarautar Katsina ta ba Hakimai da kuma Dagatai cewar su tabbatar da duk yaran da suka kai shekarun shiga makaranta, an sa su..
Ya ci gaba da bayanin cewar “ Iyaye ya kamata a taimaka masu saboda su sa ‘ya’yansu a makarantu na gwamnmati,”.
Ya bayyana cewar lokaci ya yin a gaba daya yara maza da mata suma a basu tasu damar su samun ilimi saboda su samu rayuwa mai inganci.
Sarkin ya yi kira ga Iyaye suma su taimaka ma’ya’yansu wajen samun ilimi na saboda su kasance masu dogaro da kansu.
Kabir ya kara bayyana cewar yara a lokacin da suke da kananan shekarun su, su kuma koyi sana’oi, wadanda za su taimaka masu su kasance masu dogaro da kansu, idan sun girma.
Daga karshe su ma ‘ya’yan ya kamata su ma kada su manta da irin sana’oin da ake dasu na gargajiya kamar kira kitso, da kuma rini da kuma jima.

Exit mobile version