Mai martaba Sarkin Koton karfe (Ohimege Igu), Alhaji Abdulrazak Gambo Isah Koto, ya kaddamar da ajujuwan karatu shida a makarantar yaran yan sanda da kuma wasu ajujuwan shida a makarantar sakandiren yan mata da ke garin Koton karfe a jihar Kogi, ranan asabar daya gabata.
Ofishin babban mai bai wa shugaban kasa shawara akan shirin raya muradi mai dorewa (SDG) ne, ya bada kwangilar ayyukan,amma kuma Alhaji Hassan Shu’aibu Ohimozi ne yayi sanadiyar bayar da kwangilar ayyukan a makarantun biyu.
Sarkin na Koton karfe ya yabawa Alhaji Hassan shu’aibu Ohimozi a bisa yin amfani da damar da ya samu na kawo ci gaba a yankin.
Ya kuma yi amfani da bikin wajen kira ga yan asalin yankin mazansu da matansu masu hannu da shuni da suyi koyi da Alhaji Hassan Ohimozi, sannan ya yaba masa a bisa kaunar yankin.
Alhaji Abdulrazak Isah Koto ya kuma nanata bukatar zaman lafiya a yankin,inda yace ko kadan babu yadda za a samu ci gaba mai ma’ana sai da zaman lafiya mai dorewa, sannan ya bukaci jama’ar masarautarsa dasu ci gaba da zaman Lafiya da junansu don amfanin yankin.
Da ya ke jawabi a wajen bikin, Alhaji Hassan Shu’aubu Ohimozi,wanda shine salsalar samar da ayyukan biyu, yace a matsayinsa na malamin makaranta, yayi farin ciki matuka gaya ganin cewa shirin na SDG ya wanzar da ayyukan a yankin daya fito.
Daga nan ya yabawa ofishin shirin SDG a bisa samar da ayyukan, sannan yace zai ci gaba da yin bakin kokarinsa wajen ganin ya kawo ayyukan ci gaba zuwa al’ummarsa, inda ya kara da cewa nan da yan kwanaki masu zuwa za a samar da cibiyar kiwon lafiya a kauyen Edagaki da ke yankin na Koton karfe.
Shi ma a nasa jawabin, Alhaji Usman Audu Shu’aibu wanda ya wakilci babban mai bai wa shugaban kasa shawara akan shirin SDG,yace Alhaji Hassan Ohimozi ne kashin bayan gina ajujuwan, kana ya jinjina masa a bisa kishin al’ummarsa.
Haka shi ma da ya ke jawabi, mai bai wa gwamna Yahaya Bello shawara akan shirin SDG, Alhaji Nasiru Isah Ohiani yace ayyukan sun zo dai dai akan lokacin da a ke bukatansu, sannan ya bukaci al’ummar yankin da su kare da kuma kula da ayyukan biyu.
A jawabansu dabam dabam, shugaban makarantar yaran yan sanda da na makarantar sakandiren yan mata wadanda makarantunsu ne su ka ci gajiyar shirin na SDG, duk sun jinjinawa kokarin Alhaji Hassan Shu’aibu Ohimozi a bisa yin amfani da damarsa wajen janyo ayyukan zuwa makarantunsu.
A kan haka nema su ka yi kira ga yan asalin karamar hukumar ta Koton karfe wajen ganin sun yi koyi da Alhaji Hassan Shu’aibu Ohimozi wanda a cewarsu mutum ne wanda keda kishin yankin daya fito.