Hamza Bello">

Sarkin Musawa Alhaji Muhammad Gidado Usman: Ba Rabo Da Gwani Ba

Dukkan rai za ta dandana mutuwa: wannan wata aya ce da duk wani mai rai ya tabbatar da aukuwar ta, amma abin da yake a boye a gare mu shi ne lokaci da wurin da Allah zai dauki rayuwar namu, yadda muka gudanar da rayuwar mu a zaman da muka yi a gidan duniya yana da matuka tasiri da yadda al’umma za su karbi labarin rasuwar namu. Mutum za iya fahintar haka ne in ya lura da yadda al’umma suka girgiza tare da shiga alhini a lokacin da aka sanar da rasuwar Marigayi Sarkin Musawa Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman a ranar 2 ga watan Satumba 2020, ya rasu ne bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, abin da ya fara fado mani a rai shi ne irin yadda ya gudanar da raywuarsa, yadda ya yi matukar tasiri a rayuwar al’ummarsa a matsayinsa na jagoran al’umma da kuma yadda ya shinfida adalci a zamansa na Sarkin Musawa daga cikin zuriyyar Sarkin Katsina Muhammadu Dikkko. Ya yi tsayin daka na ganin ya rike kowa a mastayin uwa daya uba, ya kuma rike zumunci ta hanyar zama jagora ga zuriyyar gidan da ke mulkin masauratar Musawa da kuma tsatson Sarkin Katsina Muhammadu Dikkko, wanda shi ne ya fara sarautar Katsina daga zuriyyar Sullubawa, marigayin kuma jika ne ga Sarkin Kano Marigayi Abdullai Bayero, tabbas ya bar tarihi na yadda ya hada kan zuriyya da al’ummar yankin Musawa a duk inda suke a fadin tarayyar kasar nan da ma duniya baki daya.

Haka kuma Marigayyin shi ne kuma babban yaya ga shahararen Malamin tarhin nan na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Margayi Dakta Yusuf Bala Usman, ya kuma rasu ya bar kannensa hudu sun kuma hada da Hon. Ahmadu Usman Liman dan majalisa wakila mai wakiltar mazabar Musawa/Matazu da Hajiya Halima Abdulkarim Usman, da Alhaji Ado Usman Liman na ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina da kuma Hajiya Bilkisu Garba Usman.

Tabbas rasuwar marigayi Sarkin Musawa, Muhammad Gidado Usman Liman zai haifar da babbar gibi babba, amma in muka kuma yi tafakkuri da cewa, marigayin ya yi tsayin daka wajen tarbiyar da al’ummar da suke tare da shi kuma bai boye dukkan sirrorin ilimi da matakan mulki da ya gada daga Kaka da Kakanni ba, wanda hakan ya sanya kowa ka gani a cikin zuriyyar gidansa za ka samu mutum ne da ya san abin da yake yi akan haka sai mu mika godiya ga Allah akan cewa, lallai marigayi ya bar baya mai albarka.

An dai haifi Marigayi Muhammadu Gidado ne a ranar Lahadi 20 ga watan Yuni 1943 (yana da shekara 77 ke nan Allah ya yi masa rasuwa), ya yi karatun allo a hannun Malaminsa marigayi Malam Iro Mai Mazuru a cikin garin Musawa a shekara 1950 zuwa 1954, daga nan ya halarci makarantar Elemantary dake Kankiya a shekarar 1955, daga nan ne kuma aka zarce da shi makarantar Firamare dake garin Minna ta jihar Neja a shekarar 1956 zuwa 1957, bayan ya kamala karatun Firamare ne ya wuce makarantar Sakadire da ke garin Suleja ta jihar Neja a shekafar 1958, lokacin da aka daukaka darajar makarantar zuwa babar makaranatar Sakadire sai ya cigaba da karatunsa na a Sulejan a shekarar 1963, bayan ya kammala karatun ne sai kuma ya wuce makarantar horas da malamai ta Bauchi, wannan kuma bayan ya samu gaggarumin nasarar lashe jarabawar da ya yi ne na shiga makarantar, inda ya fito da takardar shaidar malanta mai daraja ta biyu (Grade 11), ya kuma halarci karatuttukan kara ilimi a ciki da wajen kasar nan a lokutta daban daban.

Cikin ayyukan da Marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Gidado ya yi a lokacin rayuwarsa sun hada da wakili a hukumar Adana Kayan Tarihi a jihar Kaduna a shekarar 1974 zuwa 1978. Sannan ya zama Babban Darakta hukumar Adana Kayan Tarihi bayan da ala krkiro jihar Kastina a shekarar 1994. Sannan ya yi shugaban hukumar kula da tsabtace muhalli ta jihar Katsina a shekarar 2005. Alhaji Muhammadu Gidado ya karbi lambobin girmamawa da kuma shedar yabo da dama. Tabbas kuma marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Gidado mutum ne mai hakuri da son cigaban talakawa. Yana kishin ganin kasar Musawa ta cigaba akan haka, yakan tsaya yaga ya taimaki talakawansa musamman akan abin da ya shafi kare hakkin al’ummar.

Haka kuma tarihi ya nuna cewa, Marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Gidado Shi ne shugaban masarautar karamar hukumar Musawa tun shekara ta 1965 zuwa lokacin rasuwarsa. Ya yi wakilci a hukumar mulkin karamar hukumar Dutsinma a shekara ta 1970 zuwa ta 1974 da karamar hukumar Kankia a shekarar 1974 zuwa 1975. Ya yi wakili a hukumar kula da ilimin jihohin  Arewa ta tsakiya daga shekarar 1970 zuwa ta 1974.

Bayan an nada shi Sarkin Musawa, Alhaji Muhamadu Gidado, ya yi kokarin ganin cewa an bunkasa harka noma sosai ta hanyan tabbatar samun takin zamani da sauran abubuwa da za su bunkasa harkokin  noma da bunkasa abinci a garin yankin Musawa.

A bangaren lafiya, a zamanin sa ne aka gina asibitin garin Musawa, da wuraren shan magani a dukkanin garuruwan magaddai da wasu kauyukan dake a kasar Musawa. Sannan a zamanin sa ne aka hada garin Musawa da wutar lantarki sannan kuma aka gina mata babban Dam Kuma an samar da hanyoyi da ta taso daga Charanchi da zuwa Kafinsoli zuwa Matazu zuwa Musawa da ta bulle zuwa Kurkujen, kuma wannan hanya ta kara bunkasa tattalin arzikin alu’mmmar kasar Musawa, tabbas an samu karuwar arziki a fannonin rayuwar al’umma da dama.

Ganin irin yadda marigayin ya yi aiki tukuru na bunkasa jihar Katsina da ma yankin arewacin kasar nan gaba daya, ya kamata gwamnatin jihar Katsina a karkashin Alhaji Aminu Bello Masari ta samar da wani dandamali da za a cigaba a tunawa da ayyukan alhairin da ya gudanar a lokacin rayuwarsa, ta haka matasa masu tasowa za su amfana da darussan da ke tattare da rayuwar Marigayi Sarkin Musawa Muhammadu Gidado.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya biyu mata, Hajia Binta Lawal Aliyu da Hajia Maijidda Nasiru Maska da kuma jikoki 10, uku, muna addu’ar Allah ya albarkaci dukkan abin da ya bari ya kuma ba mu hakurin jure rashin. An dai yi jana’izarsa ne da misalin karfe 5 na yamma a gidansa da ke unguwar Sabon Gari a garin Musawa ta karamar hukumar Musawa. Muna kuma addu’a tare da fatan Allah ya gafarta masa ya kuma sa aljanna ce makomarsa.

Exit mobile version