Ammar Muhammad" />

Sarkin Musulmi Ya Bude Sabon Masallaci A Maiduguri

Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III a yau Juma’a, ya bude sabon babbar Masallacin Juma’a wanda ya ci miliyoyin kudi a garin Maidugurui. Masallacin wanda gwamnatin jihar Borno ta gina.

Sarkin Musulmi ya jagoranci daruruwan Masallata a yau din wanda suka yi sallar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa; an fara aikin gima Masallacin ne tun 1986, sai yanzu Gwamna Kashin Sheetima ya gima Masallacin bayan shekaru 33 da watsar da aikin Masallacin.

Sarkin Musulmi ya tabbatar da cewa; zai je duk nisan waje domin yada sakon Musulunci, inda kuma ya yi kira ga al’umma da su rika mutunta juna.

Exit mobile version