Mai Martaba Sarkin Nasarawa Alhaji Ibrahim Jibrin, ya yi kira ga ’yan siyasa da su ji tsoron Allah yayin gudanar da harkokin su na siyasa.
Basaraken ya yi wannan kira ne ranar Juma’ar da ta gabata a fadarsa da ke karamar Hukumar Nasarawan Makama Dogo, lokacin da ya karbi bakwancin Sanata kuma dan takarar kujerar Majalisar dattawa a Nasarawa ta Yamma, Sanata Abdullahi Adamu, Ciroman Keffi.
Ibrahim Jibrin ya ja hankilin al’ummarsa, musamman yan takarkarun gami da zabe da ke tafe, ya kuma umurce su da su gujewa gaba da habaici da kuma siyasar batanci Wanda a cewarsa, tana haddasa fitina da rarrabuwar kawunar al’umma.
“Zabe ba a yi rai ko a mutu bane. Dole a yi taka tsatsan kuma a sa tsoron Allah cikin lamarin don shi ( Allah) ya ke bada mulki ga wanda ya so”, inji shi.
Karamar Hukumar Gabasawa Gidan APC Ce – Garun Danga
Daga Ibrahim Muhammad, Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa, Hon. Mahe Garba...