Daga Bala Kukkuru,
Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Umar Ciromawa, dake karamar hukumar Garin-Malam a jihar ta Kano, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta kara damara wajen cigaba da gyaran harkokin noman kasar nan.
Alhaji Yusuf ya bayyana halan ne a gidansa da ke ciromawa cikin jihar kano a lokacin da wasu kananan manoma na jihar kano suka kawomasa ziyarar ban girma tare da neman shawarwari a gare shi bisa yadda za su cigaba da tafiyar da harkokin noman kasar nan.
Ya cigaba da cewa, tunda sun samu sa’a a Gwamnati mai ci yanzu a karkashin jagorancin adalin shugaban kasa Buhari, Gwamnati ce mai son talakawa da sauran al’ummar kasa su yi noma. Wannan nema ya sanya manoman kano suka fito suka tashi tsaye wajen gudanar da harkokin noma ahjihar kano da kewayanta baki daya.
Ya ce, ina rokon Gwamnati jihar kano da ta tarayya dasu gyara masu farashi tare da Samar da ingantaccen takin zamani kuma ya wadaci manoman jihar kano da Nijeriya baki daya, sannan kuma ya shawarci ‘yan kasuwar jihar kano da sauran jihohin kasar nan dasu cigaba da gudanar da harkokin kasuwancin su a cikin adalci tare da nuna tsoron Allah a kowane lokaci, acewar sa tun da suma ‘yan kasuwar suna da muhimmiyar rawar da zasu taka wajen kawo karshen wannan al’amari haka zalika ya cigaba da tsokaci bisa shuwagabannin kasuwar ‘mile12 Intanashinal market’ a karkashin jagorancin shugaban kasuwar Alhaji shehu usman jibirin samfam dallatun Abeokuta bisa koklkarinsa na kafa kwamiti na musamman mai dauke da mutane goma sha daya a karkashin jagorancin Babban sakataren kasuwar ta mile12 Alhaji Idiris Balarabe legas, kuma ya turosu arewa domin suzo su jajantawa manoma bisa asarorin da sukeyi na kudi, wasu kuna sukayi asarar rayuwar su baki daya, da fatan Allah ya saka masu da Alheri.
A karshe ya Isar da sakon ta’aziya ga Gwamnatin jihar kano da karamar hukumar bebeji bisa rasuwar zabeb ben shugaban karamar hukumar ta bebejin jihar kano, Alhaji Aliyu na madi wanda Allah yayi masa wa’adi a ranar lahadin da ta gabata, da fatan Allah ya jikan sa da rahama, su kuma iyalan sa Allah yabasu juriyar zaukar nauyin wannan rashi da suka yi.