Sarkin Noman Jihar Kano Ya Bukaci Gwamnati Ta Tantance Manoma Na Gaskiya

Sarkin noman jihar Kano Alhaji  Yusuf Nadabo Chiromawa ya yi kira ga gwamnati da ta samar da hanyoyin tantance manoma na gaskiya da manoma na bogi wadanda ake yi wa lakabi da manoman riga.

Alhaji Yusuf Nadabo ya yi wannan kiran ne bayan kammala wani taro na allurer riga-kafin shanu wanda ya gudana a garin Kadawa cikin karamar hukumar Garunmalam.

Sarkin ya ce ganin irin yadda gwamnatin tarayya da gwanatin jiha suke ci gaba da neman shawarwari dangane da yadda Nijeriya za ta koma dogara da noma, hakan ta sa a matsayinsu na ma’abota noma tun iyaye da kakanni cewa cikin irin wadannan shawarwari shi ne cewa gwamnati ta yi taka-tsantsan wajen hulda da manoma na bogi wadanda suke amfani da manyan riguna a matsayin su ne masu ilimi na sirrin inganra harkar.

Nadabo ya kara da cewa irin wadannan shawarwari ba wai kawai suna bai wa gwamnati ba ne  domin ganin sun kare   Kambun da suke da shi na noma ba ne. Sarkin ya ce, maganace ta gaskiya ake yi ya zama wajibi su gayawa gwamnati abin da Allah ya sanar da su dangane da harkar noma saboda a cewarsa harkar noma ba harkar aikin gwmnati ko kasuwanci ba ne, magana ce ake ta naduke tsohon ciniki harkar noma ba ta bukatar alfarma. Harka ce ta idan ka iya, a gani a kasa. Saboda haka matukar gwamnati tana so ta dawo da harkar noma na hakika ya zama wajibi ta jawo masana noma na hakika.

Gwamnati ta kiyayi manoman riga, saboda acewarsa yin hakan zai jawo koma baya maimako ci gaban da ake nema.

Da yake bayani dangane da harkar tallafawa manoma, gwamnati ta rika siyen kayan amfanin gona da manoma suka noma musamman lokacin kaka tare da cikakkiyar daraja ta musamman,  saboda yin haka zai jayo  manoma da ke karkara su kara jajircewa wajen kara wa Nijeriya abincin da za ta amfana da shi a shekaru da dama da yardar Allah.

Saboda a cewarsa manoman karkara suna samun matsala wajen hulda da gwamnati, har wala yau sarkin ya yi kira ga gwamnati da ta yi kokari wajen wadata manoman kasar nan da takin zaman da zarar damina ta fadi.

Daga karshe sarkin noman ya jaddad godiyar sa gagwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da fito da wannan tsari na riga-kafin allurar shanu ya ce, ya dada fito da darajar Dakta Abdullahi Umar Ganduje a idon manoma da makiyaya, kuma wannan ya nuna  cewa Ganduje da gaske yake yi wajen kokarin farfado da harkar noma da kiwo, bisa hakan ya yi kira ga manoma da makiyaya da ke fadin jihar Kano da su kara jan damara wajen kyutata harkar noma da kiwo domin ganin an wadata kasar nan da abinci.

 

Exit mobile version