Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sarkin Numan Ya Kwanta Dama

Published

on

Hama Bachama, Honest Irmiya Stephen, Sarkin Numan mai daraja ta daya a jihar Adamawa, ya kwanta dama yana dan shekaru 66, a duniya.

Cikin wata sanarwar da jami’in yada labarai masarautar kuma mai rike da mukamin Nzobyalata a masarautar Timawus Mathias, ya tabbatar da mutuwar sarkin ga manema labarai ranar Lahadi a Yola, ya ce basaraken ya rasu ne bayan gajiruwar rashin lafiya.
Ya ci gaba da cewa basaraken ya rasu ne, sa’o’i na ranar Lahadin 28 ga Yulin 2020, bayan gajeruwar rashin lafiya a fadarsa da ke Numan.
Ya ce, “ya rasu ne bayan gajiruwar rashin lafiya, yanzu haka ana kan shirye-shiryen zana’ida ne, kamar yadda tsarin gargajiyar masarautar da ke cibiyarta a Lamurde, ya tanada.
“Homun Honest Irmiya Stephen, ya mutu ya dan shekaru 66 a duniya” in ji Mathias.
Mista Tamawus Mathias, ya kuma tabbatar da cewa sarkin ya amshi ragamar jagorancin masarautar ne a sha biyar da watan Disambar 2013, da tsohon gwamnan jihar Murtala H. Nyako ya tabbatar da nadinshi.
Haka kuma Mathias, ya tabbatar da cewa sarkin tsohon ma’aikaci ne a rundunar sojan Nijeriya, ya ce ya yi aiki a matsayin jami’in rundunar da ya zama basarake a shekarar 2012.
Mai martaba Sarki Honest Irmiya da ke a matsayin sarkin masarautar na 28, an haifeshi a ranar 6 ga Maris 1954 a garin Lagos, daga tsatson Irmiya Stephen dan sarkin garin Bumupo da Misis Lekoni Irmiya sarkin garin Kowo, karkashin masarautar ta Bachama.
Advertisement

labarai