Shugaban Majalisar Sarakunan Samarin Nijeriya, Alhaji Sani Uba Ibrahim Daura, ya kawo wa samari da sarakunan al ummar Hausawa da sauran ’yan kasuwar mazauna cikin garin Legas ziyara, domin sanin juna tare da jaddada dankon zumunci a tsakaninsu.
Sarkin samari na Nijeriya ya fara sauka ne unguwar Mile I2, inda ya ziyarci ofishin kasuwar Mile I2 Intanashinal market da ke birnin Lagos, domin su gaisa da matashi dan uwanshi kuma shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibirin Sampam, Dallatun Abekuta, kuma Ambasadan Zaman Lafiya a Jihar Ogun, wanda shi da tawagarsa su ka yi wa Sarkin Samarin kyakkyawar tarba tare da yi ma sa barka da zuwa.
Bayan sun kammala yi ma shi barka da zuwa ne shugaban kasuwar ya cigaba da cewa, babu shakka wannan ziyara da Sarkin Samari na Nijeriya ya kawo mu su sun ji dadinta kuma alheri ce ga samari da matasa da sauran al’ummar Hausawa mazauna Jihar legas, idan a ka yi la’akari da irin muhimman abubuwan da su ka kulla na cigaban al’umma da kasa bakidaya.
Yayin da ya ke nuna farin cikinsa a game da wannan kyakkyawar tarba da su ka yi ma sa, a cewarsa, ya yi fatan Allah ya saka mu su da alheri, inda ya cigaba da cewa, babu shakka ya kawo ziyara Legas ne, domin su kara sanin juna da sarakunan samari da na sauran al’ummar Hausawa mazauna Legas.
Sai ya yi fatan Allah ya saka ma sa da alheri a bisa kokarin da ya ke yi wa al’umma a kasuwar ta Mile I2.
Daga nan ne fa Sarkin Samarin ya isa Fadar Mai Girma Sarkin Al’ummar Hausawan Mile I2, inda a nan ma a ka gabatar da shi a fadar a matsayin sarautarshi ta Sarkin Samarin Nijeriya, inda Sarkin Hausawan, Malam Haruna Jibirin, ya mike ya yi ma shi barka da zuwa tare da fadin muhimmancin wannan ziyara da ya kawo a fadarshi, sannan kuma ya yi ma sa fatan alheri na komawarshi gida Daura lafiya.
Daga nan kuma Sarkin Samarin ya ziyarci wurare daban-daban na wadansu Yarabawa ’yan siyasar jam’iyyar APC. A cikinsu har da dan takarar kujerar Majalisar Wakilai, Hon. Femi Sayeed, da sauran makamantansu.
Daga nan ya karasa fadar Mai Martaba Sarkin Al’ummar Hausawan Jihar Legas gabadaya, Alhaji Sani Kabiru, inda ya samu Sarkin tare da tawagarsa ta sarakunan al’ummar Hausawa mazauna unguwanni daban-daban da ke cikin garin Legas.
A nan ma tawagar Sarkin Hausawan na Legas ta yi na’am da zuwanshi, inda a cikin har da Kwamishinan Ruwa na Kihar Legas, Akitek Alhaji Kabiru AK Daura, da sauran makamantansu.
Daga nan su ka karbi bakuncin sa da sauke shi tare da yi ma sa barka da zuwa, sannan a nan take Sarkin Al’ummar Hausawan na Legas ya mike tsaye ya cigaba da nuna farin cikinshi tare da jin dadin kokari da kulla zumunci na Sarkin Samarin Nijeriya a game da kawo wannan ziyara tashi, inda har ya yi sasanci a atsakanin wadansu kungiyoyin samari wadanda su ka dade su na gaba da junansu.
Sarkin Hausawan na Legas ya yi fatan Allah ya saka ma sa da alheri da kuma komawarsa gida Daura lafiya.