Nasiru Adamu" />

Sarkin Zazzau Na Sahun Gaba Wajen Tabbatar Da Adalci Tsakanin Al’umma In Ji  Ahmad Yaasalam 

Ranar Lahadin da ta gabata ce, maga-takardan shugaban kasuwar Yan`lemo da ke Kwangila Zariya, Malam Ahmad Dayyib (Yaasalam) ya tattauna da manema labarai a ofishinsa da ke kasuwar ta ‘yan lemo, wanda ya yi kira ga abokan kasuwancinsu da su kara kaimi wajen rike amanar dukiyar jama’a.

Malam Ahmad ya jinjinawa Sarakunan Zazzaune musamman madugu uban tafiya Dakta Alhaji Shehu Idris da Yariman Zazzau Alhji Munir Jafaru tare da shauran mukarraban Sarkin Zazzau musamman masu ruwa da tsaki wajen bai wa Sarkin shawarar gudanar da mulki da jagoranci da ya ke yi a wannan lardin, a gaskiya mudai a wannan ka suwar tamu  ba mu da wani abu da zamu ce sai sambarka da kuma mika addu`ar mu garesu tunda bamu taba samun wata barazana ba nay tashin hankli a wannan kasuwar tamu, kuma wannan munsan kariyace daga Allah tare da iya jagoranci da yake yi ga wannan lardin, in ji shi.

Hakanan yace mai martaba Sarkin Zazzau mutumne kamili mai gaskiya da rikon amana domin kuwa duke kasar nan babu wata masarautar da ta tattaro duk wata kabilar dake kasar nan wadda ba irinta a wannan lardi na Zazzau amma ba a taba samun wata kabila ta kai kokenta ba da sunan ana nuna mata wariya ba, haka nan lardin ya tattara fahimtar Addinai daban daban, shima ta wannan janibin masarautar tana zaune da kowa lafiya, kuma babu wanda ya taba kai koken ana nuna masa wariya ba, duk da kasancewar yau ana kidayar kimanin shekaru hamsin kenan da fara gudanar da wannan mulkin da yake yi a wannan lardin, kaga ko ya cancanci yabo mafia daukaka tare da addu`ar  fatan alkairi da yawancin kwana.

Exit mobile version