Balarabe Abdullahi" />

Sarkin Zazzau Ya Karrama Makarantar Farfesa Ango Abdullahi

A tsakiyar makon da ta gabata, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya karbi bakoncin malamai da kuma dalibai na makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke da cibiya a sassan Nijeriya. Makasudin wannan karramawa da mai martaba Sarkin Zazzau ya yi wa wannan makaranta shi ne na yadda mahukumtan makarantar suka sami nasarar koyar da wani dan karamin yaro dan shekara hudu karatun Alkur’ani mai Girma, a cikin shekara hudun yaron ya kuma haddace Alkur’ani mai girma baki daya.
Wani abin tausayi ga rayuwar wannan yaro shi ne, mahaifinsa ya rasu, bayan an haife shi da wata shida, shi ne mahukumtan wannan makaranta ta Farfesa Ango Abdullahi ta dauki nauyin karatunsa kyauta a wannan makaranta tare dab a shi kula na musamman na karatun Alkur’ani da aka dora shi akai.
Bayan babban daraktan makarantar, kuma Garkuwan Malaman Zazzau, Dokta Shamsuddin Aliyu Mai Yasin ya gabatar da yaron gaban mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, sai yaron ya yi karatun Alkur’ani mai girma na tsawon kimanin minti biyar,sai daraktan makarantar ya yi karin haske kan wannan yaro da kuma darussan makarantar.
Dokta Shamsuddin Aliyu Mai Yasin ya ci gaba da shaida wa mai martaba Sarkin cewar, tun da aka sa wannan yaro kuma maraya a wannan makaranta, malamai da kuma shugabannin makarantar suka fara ba shi kula na musamman na darussan da ake koyarwa a wannan makaranta baya ga ilimin zamani ya zuwa ilimin addinin musulunci.
Dokta Shamsuddin ya kara da cewar, babban burin da mahukumtan wannan makaranta ta sa a kan wannan maraya shi ne ya sami ilimin addinin musulunci da kuma na zamani da zai kai ga zama likita da yaddar mai kowa mai komi a shekaru ma su zuwa in har wannan yaro ya na raye kuma cikin koshin lafiya.
Bayan mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya saurari karatun Alkur’ani mai Girma daga bakin wannan yaro dan shekara duhu sai ya sanya ma sa albarka tare da addu’ar Allah ya raya shi.
Salanken Zazzau Dokta Bello Abdulkadir wanda ya karanta jawabin mai martaba Sarkin Zazzau,ya kuma yaba wa mahukumtan makaranta ta Farfesa Ango Abdullahi, na yadda suka tashi tsaye wajen samar da ingantaccen llimin addini da kuma na zamani ga matasa maza da mata, sai mai martaba Sarkin ya ce ya na fatan sauran makarantu za su yi koyi da wannan makaranta wajen kula da yaran da suka rasa iyayensu, na ganin su ma sun sami ilimi mai inganci, kamar yadda yaran da ke da iyaye ke samu.
A karshen wannan karramawa da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi wa wannan makaranta ta Farfesa Ango Abdullahi, ya kuma mika wa mahukumtan makarantar takardar shaida da ya sanya wa hannu da ke alamta ya gamsu da gudunmuwar da makarantar ke bayarwa a fagen ilimin addini da kuma ilimin zamani.

Exit mobile version