Abba Ibrahim Wada" />

Sarri Ya Kusa Zama Kociyan Juventus

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus tana dab da bayyana sunan mai koyarwa, Mauricio Sarri, a matsayin kociyan kungiyar bayan da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana cewa bazata hana mai koyarwar tafiya ba idan ya nuna cewa yanason barin kungiyar ta landan.

Sarri, mai shekara 60 a duniya ya lashe gasar cin kofin Europa da kungiyar Chelsea sai dai tun farkon fara kakar wasa wadda ta gabata aka fara rade radin cewa zai iya barin kungiyar sakamakon sabani da suka samu da masu ruwa da tsaki a kungiyar.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana cewa kociyan  nata zai iya barin kungiyar saboda yanada damar yin hakan sai dai duk kungiyar da zai koma sai an biya Chelsea kudin fansa wanda yakai kusan fam miliyan biyar.

Bayan rashin jituwar da aka samu tsakanin Sarri da Chelsea tun farkon fara aikinsa, wani dan jarida Tancredi Palmeri ya bayyana cewa tuni Mauricio Sarri ya amince zai koma kungiyar Juventus a kaka mai zuwa.

Tuni dai aka bayyana cewa Sarri ya gama kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Juventus sai dai dole akwai bukatar Juventus ta biya Chelsea kudin fansa wanda yakai kusan fam miliyan biyar kafin a kammala yarjejeniyar tsakanin kungiyoyin biyu.

Juventus dai tafi son daukar mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, sai dai abune mai wahala hakan ta tabbata bayan da wakilinsa yace kociyan, dan kasar Sipaniya zai cigaba da zaman Ingila ne.

Exit mobile version