Sata Ta Saci Sata: Mai Garkuwa Ya Fanshi Kansa Akan Miliyan N1.5

Mia Garkuwa

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Wani mai satar mutane mai suna Mohammed Ahmadu ya biya Naira miliyan 1.5 don kwato ’yancinsa daga wani mai satar mutane, Abubakar Umaru a.k.a Buba Bargu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Frank Frank Mba, ne ya bayyana hakan yayin da yake baje kolin masu garkuwar tare da wasu masu aikata laifuka a Abuja a jiya.

Ya ce Buba ya yi kaurin suna wajen satar mutane a kan manyan titunan da ke kewayen Abuja. A cewar Mba, Buba shi ne na uku a kwamandan masu garkuwa da mutane wanda wani Buji ke jagoranta, mutumin da ‘yan sanda suka kashe shi tare da na biyun. Buba ya zama shugaban kungiyar ‘yan fashin kuma ya yi kaurin suna wajen kashe wadanda aka sace.

An sace Ahmadu ne a lokacin da ya zo maboyarsu a cikin dajin don sayar wa kungiyar da harsasai masu rai. Mba ya ci gaba da cewa, lokacin da Ahmadu wanda aka sace ya yi jinkirin biya, an harbe shi a hannu har sai da ‘yan kungiyarsa suka biya kudin fansa.

Ahmadu ya yi ikirarin cewa akwai lokacin da kungiyarsa ke yin garkuwa da mutane 20 a lokaci guda kuma ya adana har Naira miliyan 15 daga munanan ayyukansa. Ya kara da cewa ya ga yadda aka yi wani aiki inda Buba ya yi garkuwa da mutane 55 daga wata motar bas mai tsada a lokaci guda.

Mista Mba ya ce Ahmadu ya yi alfahari cewa yana da layu kuma ba za a iya harbe shi ba. Buba ya harbe shi don nuna yadda yake da tsanani. Ya kuma ce an san Ahmadu da “Tabbatas” saboda ya kasance sanannen mai yawan aika wa da mutane lahira.

Exit mobile version