alimailafiyasunusi@gmail.com – 08036064695:
A yanzu babu abinda ya fi jan hankali irin maganar daliban makarantar Kagara ta Jihar Neja da wasu yan bindiga suka yi awon gaba da su, wanda har kawo yanzu babu labarin cewa an yi nasarar ceto su. Iyayensu na zaune cikin tashin hankali saboda rashin sanin takamaimai halin da suke ciki. Kwanaki kadan da suka wuce haka aka shiga makarantar kwana ta garin Kankara aka yi awon gaba da dalibai maza, duk da cewa Gwamnati ta ceto su, to amma abun yana kara ta’azzara yadda yan bindiga suka samu damar sace daliban makaranta.
A wani dare na 14 ga watan Afrilun 2014 haka yan Boko Haram suka yi awon gaba da daliban Makarantar Chibok, abinda ya ja hankalin duniya gaba daya. Hankalin kowa ya tashi saboda ganin irin karfin gwuiwar da za a ce yan ta’adda suna dashi da har za su iya sace daruruwan dalibai su yi awon gaba dashi. Wannan ya kara fito da sakaci na jami’an tsaron da suke bata-kashi da Boko haram, sannan ya kuma nuna rashin kwarin gwuiwar kawar da Boko Haram. Shekara hudu tsakani a wani yammaci na 12 ga watan Fabrairun shekarar 2018 wani ya kirani tare da tambayar shin da gaske ne yan Boko haram sun kuma yin awon gaba da daliban makarantar Dapchi, ina duba jaridun Kasar nan naga wannan mummunan labari. A takaice idan muka lissafa, an sace daliban makarantar kwana sau hudu, Dapchi da Chibok (Borno), Kankara (Katsina), sai kuma Kagara (Naija), har kawo yanzu ba’a san halin da daliban Kagara suke ciki ba, yayin da kuma har kawo yau akwai yaran Chibok da yan Boko haram basu saki ba, mafi shahara cikinsu itace Leah Sharibu.
Idan muka al’amarin ta wata sigar zamu tabbatar da shirin dake cikinsa. Tun daga kafuwar Boko haram shekaru wajen 12 har kawo yanzu, bazaka iya kirga adadin sau nawa suka kai hari wa makarantu a Kasar nan ba. Dama kuma da’awar su itace karatun Boko haramun ne a wajensu, wannan shine abinda suke so su tabbatar an dena. Duk da cewa manyan Malaman Addinin Islama tuni sunyi matsaya akan halacci da kyawun karatun zamani, don haka tun anan mun fatattaki da’awar da yan Boko haram sukeyi. Abu na farko dana fahinta shine, Boko haram sunzo ne domin takowane hali sai sun haramta mana (Arewa) muyi karatun zamani domin cigaba ta fuskoki da dama. Wannan itace babban ginshikin kafuwar Kungiyar data kira kanta da ‘Jama’a Ahl Sunna Lil-Da’awa Wal Jihad’.
Wannan shiri ne kullum na ganin an karya Arewacin Kasar nan ta fuskoki da dama. An durkusar damu tuni dama ta fuskar kasuwanci, yanzu abun ya fara komawa Kudancin Kasar nan munaji muna gani, ga kuma shirin ganin an dakile mu wajen samun ilimin zamani, wannan shirin shima gashi yana samun karbuwa saboda yadda tsoron abinda zai faru ga Yara, ya sanya wasu hakura da tafiya neman ilimin, kuma dama har kawo yanzu akwai masu ganin cewa Boko kafurci ne.
Ilimi wani ginshiki ne da yake daga darajar al’umma. Ya kuma bata cigaba ta fuskoki da dama, tun daga kan tattalin arziki, kimiyya, fasaha da kuma samun shiga a dama daku a al’amuran duniya, tare da kokarin janyo duk wani abinda zai kawo nasara ga al’ummar ka. Wannan kusan koyaushe shine fasahar dake cikin ilimin zamani. Idan muka kalli Arewacin Kasar nan, yana daya daga cikin abinda kullum ake mana gori cewar Arewa bama da ilimi, ko bama bawa yaranmu mata ilimin zamani, to amma idan ka dubi duk wani cigaba dana fada a sama, munada masu ilimin da suke kawo mana wannan cigaban, dede da kasuwancin da akeyi a Arewa, masu ilimi sun shiga sun kuma bunkasa shi. Idan ka dauki bangaren siyasa ko sha’anin Gwamnati, zakaga cewa nan ma dai ba’a barmu a baya ba, mutanen mu sunyi kakagida da kane-kane…..
Wadannan dama wasu dalilai suna cikin abubuwan da suka sanya ake shirin ruguza wannan yanki namu ta fuskoki da dama. A halin da ake ciki, Jagororin mu na Arewa ne kadai zasu tsaya Kai-da-fata wajen ganin sun kawo karshen duk wani shiri da ake akanmu. Duk wani rikici ko tashin hankali idan yafaru, zakaga cewar a Arewa ne, haka duk wata bola da shara idan aka kwaso, zakaga Arewa ne. Yanzu dai ya ragewa Jagororin mu walau su tashi tsaye, ko kuma munaji muna gani muci gaba da zama bora.