Satar Jarabawa: Tsokaci A Kan Illarsa Da Hanyoyin Magancewa 

Daga Muhammadu Sani Bello (07046415284)

Satar Jarabawa ya zama ruwan dare wanda ya addabi al’umma, musamman Nijeriya. Matsala ce da ta shafi dukkannin matakan karatu. Daga matakin firamare, sakandare, har zuwa jami’a, dukkan su basu tsira daga wannan annobar ba. Satar Jarabawa wanda a turance ake kira da “Exam Malpractice” ya shahara a makarantun Gwamnati, ya kuma gawurta a makarantu masu zaman kansu. Inda dalibai ke shiga da satar amsa cikin dakin Jarabawa domin su kwafa amsa maimakon su yi da kansu. Duk da irin jajircewan malamai na sai-ido, amma abin na cigaba da ci kamar wutar daji.

Satar Jarabawar na iya daukan salo daban daban. Ya danganta da irin kawarewar wanda yake satar jarabawan (abun ban dariya) . Zan kawo kadan daga ciki domin nemo hanyar magancewa.

Matakin firamare; wanda daga nan dalibi ke koyon wannan mummunar dabi’a. Misali, salon satar Jarabawan da ya yi shuhura a wannan matakin shi ne; dalibi ya tambayi abokinsa ko na kusa dashi amsa a dakin Jarabawa. Wasu lokutan malamai na ganin kaman ba wani babban al’amari bane, amma ta bayan fage kuma, shi ne babban abun da ke koya ma dalibai satar Jarabawa. Saboda idan tafiya ta yi tafiya wata rana ya waiga babu wanda zai tambaya, to babu abun da zai hana shi bude littafi, ko kuma ya shiga da wani abu da zai kwafa daga ciki. Kuma idan ba’a dauki wani babban mataki ba, to haka zai cigaba har zuwa mataki na gaba.

A wasu Makarantun (firamare), idan lokacin rubuta Jarabawan shiga sakandare ya yi wasu, malamai kan zama a kan gaba wajen rubuta ma dalibansu Jarabawan da sunan taimako. Wannan na cikin abin da ke taimaka wa dalibi wajen shiga matakin gaba da wannan bakar dabi’a.

Matakin sakandare; daga aji daya har zuwa aji na shida ( JSS 1– SSS 3) Sanadiyyar gazawa wajen magance matsalar a matakin baya shi ne babban dalilin da yasa wannan matsala ta samu wurin zama a matakin sakandare inda dalibi ke ganin ba wani babban abu bane. Kuma anan ne dalibi ke kwarewa wajen satar amsa a dakin jarabawan. Hakan na iya kai shi rubuta amsa a hannu, Takarda, jikin uniform dinshi, da sauransu. Akwai ani wabu da ya faru a kwanakin baya; Wani malami ne ya sanar da zai ba dalibanshi jarabawa, da yake kwas din yana da dan wahala, haka daliban suka dukufa da karatu dare da rana. Washegari kafin a shiga dakin Jarabawan sai da malamin ya tabbata ya caje kowa babu wanda ya shiga da littafi ko wata takarda. Abin takaici yana cikin zagayawa sai ya kama wani Dalibi na kwafan amsa a gefe rigarsa, kuma har ya yi nisa (abin dariya da ban takaici) nan Malamin ya kore shi daga dakin Jarabawar kuma ya hana shi rubutawa.

Daga cikin dalilin dake tunkuda dalibai satan jarabawa akwai ; Rashin yin Karatu. Wani sashe na dalibai sun dogara ne kawai da satan amsa, wato baza su karanta komai ba sai su shiga dakin jarabawa da littafi ko Wani abu da za su iya kwafa daga ciki. Idan kuma aka samu wani abu da ya hana sun satar amsan to sai kuma ido ya raina fata, su rasa abin da zasu rubuta. Sanadiyyar haka sai su fadi jarabawar.

Daga cikin dimbin dalilan akwai “TSORO”; dalibai a Makarantun firamare na tsoron fadi jarabawa saboda idan suka kuskura suka fadi to za su gamu da fushin iyayen su, ko kuma abokan su za su yi masu dariya. Wanda hakan ke sanya dalibi ya yi iya yin shi domin ya tsallake jarabawar, ko da satar amsa ne. Hakazalika a matakin sakandare dalibai na tsoron iyayen su, malamai, da abokan karatunsu, idan suka fadi komai zai iya faruwa. A Makarantun jami’a ko, anan ne dalibai ke gamuwa da asalin tashin hankali, kiri-kiri malami zai fada maka zai baka “Carry ober” kalmar da duk wani dalibi a jami’a ke tsoron ji harda masu baiwan karatu. Wannan ke sanadiyyar jefa dalibi wannan mummunar dabi’a.

Yakamata iyaye su kasance masu karfafa yayansu a kowani lokaci, idan suka ci jarabawa su taya su murna, idan kuma suka fadi su zauna da su su nuna masu cewa ba karshen ta ba kenan. Akwai saura a gaba. Kuma za su iya kokarin da ya wuce wannan.

Malamai kuma a jamio’i, su kasance kamar iyaye, wajen jawo dalibansu a jiki, basu shawarwari, da kuma karfafasu.

Abu na gaba shi ne “Rashin yarda da Kai” daga cikin abun dake cutar da wasu dalibai a Makarantu (kowani mataki) akwai rashin yarda da Kai, A mtsayinka na dalibi, mai son karatu, dole sai ka fara yarda da cewa zaka iya karatun, sa’annan zaka iya fuskantar duk wasu kalubale da za su shigo a harkar neman Karatun. Idan ka yarda da kwakwalwarka, ba tare da ganin gazarwarka ba, to tabbas zaka cimma abun da ka fita nema na karatu. Kar ke ce dole sai ka yi kalan abunda wani yayi koda a harkar rayuwa ne. A duk lokacin da kake kokarin kwatanta kan ka da wani, kana hankoron hawa matakin da to dole sai ka gamu da kalubale. Idan

Dole ne mu kalli wannan matsala da faffadar mahanga, saboda cikin kokarin da Makarantu ke yi wajen yaki da wannan mummunar dabi’a akwai koran duk dalibin da aka kama da laifin satar amsa a jarabawa. Babu wanda zai so a kore shi ko kuma dan shi daga Makaranta ko wace iri ce.

Babu shakka Gwamnati da Ma’aikatar ilimi, da dukkan bangarorin da ke da hannu a harkar ilimi na aiki tukuro domin magance wannan matsala.

 

Exit mobile version