Abubakar Abba" />

Satar Shanu Na Yi Wa Sana’armu Barazana – Sarkin Fawar Ado Paki

Sarkin fawa na karamar hukumar Kaduna ta Kudu Alhaji Ubale Na Ado Paki ya sanar da cewa, satar shanu a kasar nan, musamman a Arewacin Nijeriya yana janyowa sana’asr su babban kaluble.

Alhaji Ubale Na Ado Paki a hirarsa da Jaridar Leadership Ayau a Kaduna ya ce, hakan yana shafar sana’ar mu ta fawa saboda ana samun matukar karancin Shanun da zamu yanka don sayawara da alumma.

Ya sanar da cewa, wannan yana daya daga cikin babban kalubale kuma idan mun yi karin kudin naman da muke yankawa don sayarwa, sai mutane su fara yin korafi cewa, naman ya yi tsada.

Shugaban ya ci gaba da cewa, kaga a kasuwar nan ta Bacci inda muke yin sana’ar mu ta fawa, ada munfi mu kusan kashi tsasa’in, amma a yanzu zaka iya gani da idon ka ga gadaje nan babu kowa a kai,inda ya yace, wasu sun bar garin wasu suna nan a garin amma wahala ta yi masu yawa.

“Mu na kuma kira ga Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-rufai da ya turo ya sanya a duba yadda sana’ar ta fawa ta gagari wasu mahutan mu da dama saboda yana yin rayuwar yau.”

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta basu jari don mu samu mu kara mikewa da kafafun su domin duk inda kaga mahauci ba raggo bane mutum ne da ya san zafin kansa yake kuma mayar da hankali a kan sana’ar fawar don ya zamo mai dogaro da kansa har ma ya janyo wasu ya koya masu sana’ar don suma su zamo amsu dogaro da kansu.

Ya ce, “Mu ma mahauta muna bayar da tamu gudunmawar wajen yakar zaman kashe wando a tsakanin allumma musamman matasa da kuma bayar da gudunmwar mu wajen ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba.”

Da ya ke yin tsokaci akan sauran matsalolin da masu sana’ar suke fuskanta shugaban ya ce, matsalolin dai suna da dama, sai dai mu ba ku yan kadan daga cikinsu.

Ya ce, sana’ar fawa, ta samo asali ne daga lokacin Annabawa kuma sana’a ce mai kyau, saboda haka zan ba yarda ba misali, kamar a nan yankin na Kaduna ta Kudu mu Musulmi ne muka fi yawa kuma idan aka nada ka aka ce kai ne Sarkin fawa, ya kamata ka kare hakkin jama’a, musamman mata da yara da ke a gida.

A cewar sa, abin da nake nufi a nan shi ne, ka kare hakkin jama’a yadda za ka kare shigo da naman da ya lalace, ma’ana mushe, domin Allah zai tambaye ka irin ayyukan da ka yi, kuma saboda irin wadannan matsalolin ne, wasu mutane in sun je otel-otel, ba sa cin abinci da nama, ban ce manyan ote-otel ba, domin suna zuwa ne a awana masu nama su saya mun kuma san idan suke sayen nama, wasu masu karfi a cikin manyan otel-otel din har sun a sayen Shanu ana yanka masu ne.

Ya kuma yi nuni da cewa, amma irin yan kananan otel-otel akwai Shanun da Awaki suke mutuwa da bata gari suka yi mana kutse a cikin sana’ar suna sayar masu saboda suna son su samu kudi.

Shugaban ya ce, “ina kara gayawa mutane muji tsoron Allah haka suma masu sayen irin wannan mushen suji tsoron Allah karsu sanya kudi a gaba kabarin su ya kamata su duba.”

A karashe shugaban ya ce yan na kaman ba Mahauta bane kuma sune sukafi yawa suma suji tsoron Allah domin jama’a, suna a cikin wani hali na kuncin rayuwa.

Exit mobile version