Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Satar Yara: Akwai Kurakurai A Maganganun Mai  Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II

by
3 years ago
in RA'AYI
2 min read
Satar Yara:  Akwai Kurakurai A Maganganun Mai  Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, mai kowa mai komai, Wanda ya bani damar yin wannan ‘yar gajeriyar fadakar wa zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano da dukkan daukacin al’umma masu irin ra’ayin sa game da satar yara da ake tayi a kwaryar birnin jahar Kano.

Wanda sanin kowa ne,  Allah ya bawa Mai Martaba sarki baiwar ilimin addini da na zamani. Hakan kuma yana taimaka masa wajan iya gogayya da jama’a a duk fadin duniya. Amma sau da yawa sarki yana fadar gaskiya kuma tana yiwa mutane dadi. Amma a wannan jikon Sarki ya yi maganganu masu ban mamaki da ban al’ajabi, wanda muke ganin sarki ya yi tuntuben harshe ba haka ya kamata yace ba.

Ko shakka babu,  abubuwa da dama sun faru da mai martaba sarki na wajan kasa fahimtar irin ra’ayoyin shi. Wanda sau da yawa mu mukanyi uwa da makar diya wajan wayar da kan al’umma. Amma a wannan karo bama tare da sarki. Saboda yaci karo da tsarin mu’amalar rayuwa dama tsarin koyarwa ta addinin musulunci.

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

Ra’ayoyinku A Kan Yadda Manoma Za Su Fuskanci Harkar Noma A Daminar Bana

Sanin kowa ne Annabi (S.A.W) yana fada a cikin wani sahihin hadisi yana cewe ” Musulmi ya fadawa dan uwansa Musulmi magana me dadi sadaka CE”. Ni na dauka mai martaba sarki zai fada musu maganganu masu nutsar da zuciya,  ba kalaman da za su sa iyayen yara jimami ba.

Mai martaba sarki ya kamata yasan akwai bambanci tsakanin ‘Ya ‘yan talakawa da ‘Ya ‘yan masu kudi. A cikin talakawan ‘Ya yan su suna zuwa makarantu kama daga na BOKO zuwa na islama. Wanda sau da yawa yaran nan da Kansu suke tattaki zuwa wadan can makarantu sabanin abun yadda yake a gidan masu  hannu da shuni.

Ni dinnan zan iya tuno sadda muna yara muke zuwa marantar firamare da islamiyya a kafa. Wanda muke tafiyar kimanin kilomita shida (6) zuwa da dawo wa. Amma tun a lokacin ‘Ya ‘Yan masu kudi a mota ake kaisu. Saboda haka babu yadda shugaba zai zargi iyaye da laifin barin yara suna fita daga gida. Ko kadan yin hakan ba dai dai bane.

Maganar da me girma sarki yayi ka iya tsunduma iyayen yara su fada zuwa cutar damuwa da tunanunnuka (wato depression). Wanda ba karamar illa bace a garesu.

Amma inason mai karatu ya fuskanci zance na ba ina nuna iyayen yara basu da laifi ba. Suma iyayen yara ya zama dole su kula da ‘Ya ‘yan su sosai.

Muna kira ga mai martaba sarki da ya yi gaggawar bawa jama’ar jihar Kano hakuri musamman iyayen yaran da suka salwanta.

Allah ya bayyana mana su, Allah ya kiyaye gaba, ameeen.

52ND SUG PRESIDENT BUK

Level 600 Medical Student

Email: khalidsunusikani13@gmail.com

Phone Number: 07030631259

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaba Buhari Ya Taya Wazirin Dutse Murnar Cika Shekara 70 A Duniya

Next Post

Gwamna El-rufai Ya Nemi Mutanen Kogi Su Sake Zaben Yahaya Bello A Karo Na Biyu

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

‘Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

by
21 hours ago
0

...

manoma

Ra’ayoyinku A Kan Yadda Manoma Za Su Fuskanci Harkar Noma A Daminar Bana

by A’isha Seyoji
21 hours ago
0

...

‘Yan Arewa Mu Yi Biris Da ‘Yan Siyasar Da Ba Su Damu Da Kisan Da Ake Mana Ba – Matasan Arewa A Kudu

‘Yan Arewa Mu Yi Biris Da ‘Yan Siyasar Da Ba Su Damu Da Kisan Da Ake Mana Ba – Matasan Arewa A Kudu

by
1 week ago
0

...

Filato Da Taraba

Ra’ayoyinku A Kan Ahuwar Da Gwamnati Ta Yi Wa Tsofaffin Gwamnonin Jihar Filato Da Taraba

by A’isha Seyoji
4 weeks ago
0

...

Next Post
Gwamna El-rufai Ya Nemi Mutanen Kogi Su Sake Zaben Yahaya Bello A Karo Na Biyu

Gwamna El-rufai Ya Nemi Mutanen Kogi Su Sake Zaben Yahaya Bello A Karo Na Biyu

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: