Sau Uku Jirgin Sojoji Na Hadari A Cikin Wata Biyar

Daga Maigari Abdulrahman

Biyo bayan hadarin jirgin shugaban rundunar Soji, ana ta tofa albarkacin baki tare da korafi kan yawaitar afkuwar hadarin jirgin sama a Najeriya.

A cikin watanni biyar zuwa yanzu, jirgin saman rundunar Sojin Najeriya ta sama uku ya yi hadari, inda ya yi sanadiyar kashe sojoji 21, ciki har da shugaban sojin kasa, Janaral Ibrahim Attahiru.

Hakan dai, ya janyo tofa albarkacin bakin mutane, inda wasu ke saka alamar tambaya kan kwarewar matuka jirgin, da kuma bangaren ma’aikatan jirgin saman sojin.

Daga 2015 dai, rundunar Sojin saman ta yaye matuka jirgi 118.
A watan Febrairu, 20 ga wata, jirgin sojin ya yi hadari yayin da yake dawowa daga Minna zuwa Abuja daga wani aiki, inda sojoji bakwai din da ke ciki su ka mutu gabadaya.

A 1 ga watan Aprilu kuma, wani jirgin Sojin dauke da mutum biyu ya bace bat, har yau ba a samu labarin sa ba.

Sai dai, wani babban jami’in soja, ya ce hadarin jirgin sama ba bakon abu ba ne.
Babban jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce jiragen Sojoji kan yi hadari a ko’ina, a wasu kasashen, don haka bai kyautu yada zarge-zarge ba.

“A Amerika ma jiragen Sojoji kan yi hadari, haka ma a wasu kasashen. Jirgi wani abu ne da ba za ka iya kula da shi ba dari bisa dari. Dan haka hadarin jiragen ba wani abu ba ne. Mun damu da lamarin, muna fatar hakan ba za ta faru ba nan gaba,” in ji shi

Exit mobile version