Saudiyya Ta Amince ‘Yan Kasashen Waje Su Je Aikin Hajjin Bana

Za a bar maniyyata daga fadin duniya su je aikin Hajji a wannan shekarar, tare da tabbatar da bin tsauraran dokokin domin kiyaye yaduwar Korona a masarautar, kamar yadda wani rahoton jaridar Al-Watan ta rawaito.

Wannan matakin na zuwa ne bayan hukuncin da hukumar Hajji da Umara ta kasar ta yanke a ranar 9 ga watan Mayu cewa ya kamata a bar mahajjata su yi aikin amma da sharudan hukumomin lafiya.

A farkon wannan watan ne, ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta ce za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kiyayen lafiyar duk wanda ya je aikin ibada a kasar.

Sai dai ma’aikatar ta ce za ta sanar da hanyoyin kare kai da za a bi domin kiyaye yaduwar Korona daga baya.

Musulmi sama da miliyan 2.5 ne ke zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji a ko wacce shekara daga fadin duniya, amma saboda annobar Korona a ka rage adadin zuwa 1,000 a bara.

Exit mobile version