Saudiyya Ta Cafke ‘Yan Gidan Sarauta 11

Ministan shara’a Saudiya ya bayyana cewa jami’an tsaro sun capke yan gidan sarauta 11 da aka kama a lokacin da suke gudanar da taron nuna adawa da matakin tsuke bakin aljihun da hukumomin kasar suka aiwatar.

Mutanen da aka kama sun gudanar da wannan gangami ne a harabar fadar sarkin dake birnin Ryad.

Ministan Shara’ar kasar Saud Al Mojeb ya bayyana cewa masu zanga-zanga sun bukaci hukumomin kasar da su biya su hakin su bayan hukuncin kisa da aka yankewa daya daga cikin yan gidan sarauta da aka yamkewa hukunci kisa shi a shekara ta 2016.

Exit mobile version