Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa, saura kiris matsin tattalin arziki wanda cutar Korona ta haddasa ya tafi daga Nijeriya. ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed shi ya bayar da wannan tabbaci a ranar Litinin a Jihar Legas wajen taron manema labarai na sabuwar shekara.
A karshen wata shida na shekarar 2020, Nijeriya ta fada cikin matsin tattalin arziki bayan da ta samu karancin samun kudaden shiga a wata hudun na shekarar 2020.
“Saura kiris wannan sabon matsin tattalin arzikin da Nijeriya take fuskanta ya kau, ba zai dauki tsawan lokaci ba kamar yadda aka fuskan a shekarar 2016 wanda ya kwashe tsawan watann goma.
“Saboda gwamnati ta kammala shirye-shiryen kudade da za su dakile lamarin tare da samun damar farfado da tattalin arziki wanda ya kurkushe sakamakon cutar Korona,” in ji ministan yada labarai da al’adu.
Ministan ya daura alhakkin jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arzikin a kan cutar Korona wacce ta durkusar da ayyukan tattalin arzikin Nijeriya. Y ace, kasashen da suka ci gaba irin su Amurka da Burtaniya da Kanada duk sun fuskanci matsin tattalin arziki a lokacin cutar Korona. ya kara da cewa, sauran kasashen da suka fuskanci matsin tattalin arziki sun hada da Austria da Belgium da Denmark da Estonia da Finland da Hungary da Ireland da Italy da Latbia da Lithuania da Medic da Netherlands da Norway da Romania da Russia da kuma Spain.
Ministan ya jaddada cewa, matsin tattalin arziki ya yi matukar shafar ci gaban kasar nan.
“A cewar hukumar kididdiga ta kasa, an samu raguwar tattalin arziki na kashi -3.62 a wata shidan shekarar 2020, yayin da aka samu na kashi -6.10 a wata hudun shekarar 2020.
“A yanzu yanayin ayyukan tattalin arziki suna karuwa wadanda suka zarce 17, idan aka kwatanta da na wata hudun shekarar 2020 wanda ake da 13.
“Kashi -3.62 na watan hudun shekarar 2020 da kashi -6.10 na wata shida kamar yadda hukumar kididdita ta ce an samu raguwarsu a cikin ayyukan tattalin arziki sun hada da na cikin gida Nijeriya ne da kuma na kasashen ketare na,” in ji shi.
Mohammed ya ce, kafin zuwan cutar Korona, tattalin arzikin Nijeriya ya samun nasarar ci gaba a duk wana a shekarar 2020, amma tun daga lokacin da cutar Korona ta bullo, yake fuskanci matsaloli masu yawa. Ya ce, sakamakon haka ne aka samu matsaloli a bangaren mai wanda ya haddasa faduwar farashin mai a kasuwan duniya. Ya ce, matsalar da ta tsaya a bangaren mai ba kadai sai da ta shafi sauran fannoni tattalin arziki wadanda ba na mai ba.
Mohammed ya ce, mutane da dama sun manta da matsalolin tsaro da kasar nan take fuskanta a baya wanda kuma lamarin ya hade na tattalin arziki. Minista ya ce, mun gode wa Allah da ya sa aka yi murnar Kirsimeti da na sabon shekara ba tare da tashin bam ba. Ya ce, a shekarar 2010 da shekarar 2011 da shekarar 2012 duk a ranar murnar Kirsimeti sai an farmaki mutane wanda ke janyo rasa rayuwa daruruwan mutane da kuma dokiyoyi. Haka kuma, Mohammed ya ce, a watan Agustan shekarar 2011, aka saka bam a ginin Majalisar dinkin Duniya da ke Abuja da wanda aka saka a watan Afrilu shekarar 2012 da kuma wanda ya kashe dalibai 40 a garin Mubi Jihar Adamawa wanda aka saka a watan Oktobar shekarar 2012. Ya ce, bincike ya nuna cewa garuruwa guda 80 aka farmaka tare da banka wa kauyuka wuta da mayakan Boko Haram suka yi a baya.