Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Gareth Bale ya bayyana cewa akwai magana a baya ta cewa zai koma Manchester United, sai dai daga baya abubuwa suka canja.
Mai koyar da kungiyar Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana sha’awarsa ta daukar dan wasan a wannan kakar, inda ya ce yana son dan wasa kamar Bale domin ya cike adadin ‘yan wasa hudu da ya yi niyyar dauka bayan da ya kasa sayen Iban Perisic daga Inter Milan.
“Tabbas an yi maganar komawa ta Manchester United, sai dai na yi tunanin adadin kofunan da na ci a baya a Madrid, hakan ya sa na canja shawarar zama a kungiyata.” In ji Bale.
Rahotanni dai sun ce United za su koma neman dan wasan a kakar wasa mai zuwa indai ya yi kokari sosai.