Ba don an gaggauta daukar matakan da suka dace ba, da sai dai mu ce saura kiris ya rage Nijeriya ta kone; konewa kurmus kuwa. Ba don rufin asiri irin na Allah ba, ba kuma don an sa dattako da kai hakali nesa ba, ba domin daukar matakan yawaita jami’an tsaro ba, dai tuni labari ya canza.
Da an tafka kuskuren sakaci, kamar yadda gwamnatocin baya suka yi ta tafkawa. Da lamarin sai ya fi na rikice-rikicen da aka yi ta gwabzawa a Kaduna, Filato, da sauran jihohin da suka shahara da rikici da tashin hankali.
A shekarun baya, an shaidi jihohin Filato da Kaduna da kaurin suna a rikice-rikicen addini da kabilanci. Wannan wani lamari ne da babu wanda yake fatan sake ganin afkuwar makamancinshi. Saboda yawan rayukan da suka salwanta, da irin tarin dukiyar da aka yi asarar ta.
Da zaran wani lamari na tashin hankali, ya kunno kai a Nijeriya, garuruwan nan biyu ake shakkar su fara kamawa da wuta. Saboda suna kamawa, kurmus suke yi. Sai dai akwai bambanci tsakanin jihohin da Jihar Kano.
Musamman ma idan ya kasance a rikicin, cuta ko zaluntar hausawa ake yi. Wannan ne irin annobar da ake tsoro ta kunno kai. Saboda da zaran al’umman Kano sun dau haramar ramuwar gayya, kowa sai ya ji a jikinsa.
Cikin ikon Allah, da guguwar rikicin Biyafara ta kunno kai, sai gwamnatin tarayya da ta jiha, hard a masarautu suka yi gaggawan daukar matakin kiyayewa. Har ta kai ma a makon da ya gabata, mun ruwaito hudubar Sarki Sanusi II, inda ya yi kira da a kamo wadanda suka aikata aika-aika akan hausawan da ke Kudu. Amma kuma ya gargadi al’ummarsa das u kauracewa duk wani nau’in ramuwar gayya. Domin dirarwa wani ko wasu gungun mutane ba tare da hakki ba.
Duk ya zama tilas mu yabawa matakan gwamnati da masarautu bisa rawar da suka taka wurin dakile yaduwar annobar rikicin ‘yan biyafara, amma fa wadanda suka fi dacewa a yaba tare da jinjinawa sune al’umman kasar Hausa. Mutanen Kano sun nuna karamci, sannan su nunawa al’ummar Nijeriya da duniya cewa su mutane ne masu aiki da hankali ba rashin hankali ba.
A makon da ya gabata, an dauko labaran yadda hausawa suka yi shiga irin na Ibo a Kano, suka yi gangamin zaman lafiya. Wannan kadai ya ishi amsa ga duk wanda ke tunani ko mafarkin cewa ta kowanne hali sai ya kona Nijeriya. Wadanda ake son, tunzurawa domin su yi aika-aika, sun ki, maimakon hakan ma, sai suka nuna cewa su masu hankali ne.
Ba don mutanen Arewa sun kai hankali nesa ba, da tuni burin makiyan Nijeriya ya cika. Da maimakon yanzu mu rika bayar da labarin dattako, sai dai mu rika ruwaito labaran irin asarar da aka tafka, da irin rayukan da suka salwanta. Wannan shi ma idan mun kai labara, hargitsi bai ruwtsa da mu ba kenan.
Tabbas, lamarin biyafara day a kunno kai, saura kiris ya shafi kowa. Kuma kiris ya rage kowa ya ji a jikinsa. Domin wannan karon ya saba da shekarun baya da aka gwabza yaki tsakanin gwamnatin Nijeriya da rundunar ‘yan ta-ware na Ojukwu.
A wannan jikon, an riga da an samu cudanya tsakanin kabilun arewa da kabilun kudu. Barnar sai tafi tayar da hankali, fiye da ta wancan shekarar.
Ya na da kyau gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta ci gaba da daukan matakan da take dauka na dakile yiwuwar afkuwar ire-iren wadannan matsaloli. Ko ba komi gwamnatin tarayya da ta jihohi sun kokarta matuka wurin takawa rikicin da ya kunno kai cikas.
Fatanmu shi ne Allah ya ci gaba da kiyayewa, tare da kare mu daga mugun ji da mugun gani. Masu nufin al’ummanmu da sharri kuma, Allah ya mayar kawunansu.