Yusuf Shuaibu">

Saurayi Ya Kashe Ubangidansa Don Ya Hana Shi Kawo Mata

Wani matashi dan shekara 21, Nonso Umeadi Oyiboka, ya shiga hannun rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Anambara bisa zargin dabawa mai gidansa wuka har lahira a Ogidi Ani-Etiti da ke karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Haruna Mohammed, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, an kama wanda ake zargin ne a ranar, bayan wani rahoto na zargin kisan mai gidansa, Nonso Umeadi Oyiboka, mai shekara 35.
An tattaro cewa, mamacin ana zargin ya dan sami sabani kan “kawo mata da yawa a cikin gidan da yaron ke yi” wanda daga karshe ya haifar da rikici da ya kai ga kashe mamacin har lahira.
Wanda aka kashe din, wanda an yi ta daba masa wuka da yawa a bayansa, inda aka gardaya da shi zuwa bayan da aka tabbatar da mutuwarsa a can.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP John B. Abang, ya ba da umarnin a tura karar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (CID) don gudanar da bincike cikin hikima bayan haka za a gurfanar da wanda a ke zargin zuwa Kotu don fuskantar hukuncin da ya dace da shi.

Exit mobile version