Ahmed Muhammed Danasabe" />

Saurayi Ya Rasa Ransa A Rikicin Kungiyar Asiri A Lokoja

A ranar Juma’a da misalin karfe 10 na dare ne wani matashi mai suna Ndagi Idris Muhammed, dan shakara 20, ya rasa ransa a wani kazamin fada da ya barke tsakanin kungiyoyin matsafa biyu a Unguwar Kabawa da ke birnin Lokoja.

Lamarin mara dadi ya tada hankulan al’ummar unguwar wadanda suka ce hakan shine karo na hudu irin wannan lamari na faruwa.

Yanzu haka dai wanda ake zargi da kashe Ndagi,mai suna Shaibu ( Shapiro)  ya ranta na kare kuma jami’an yan sanda da yan sintiri na unguwar sun baza komarsu don kama shi.

Wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU wanda ya ziyarci gidan marigayi Ndagi don yiwa yan uwansa ta’aziyya game da rashinsa,ya kuma samu zantawa da iyayen marigayin wadanda suke cikin tsananin alhini da jimamin rasuwar dan nasu.

Maihafin marigayin,wato Mallam  Muhammed ya shaidawa wakilinmu yadda lamarin ya faru da kuma irin yadda yaji a lokacin daya samu labarin rasuwar dan nashi. Yace Ndagi wanda saura yan watanni a yaye shi a wajen koyon kanikanci ya sallame shi da sanyin safiyar ranan da lamarin ya faru da zimmar zashi wajen koyon aikinsa na kanikanci,inda ya kara da cewa kafin marigayin Ya bar gida zuwa wajen aiki, sai daya ya ba shi kayansa ya wanke masa, daga bisani kuma ya sake aikensa ya sayo ma sa ‘recharge card’.

“Ina zaune da misalin karfe takwas na dare bayan na dawo daga masallaci, sai na samu labari a wajen yara cewa wasu yan kungiyar asiri biyu suna rigima a cikin unguwarmu( Kabawa). Bada dadewa ba, sai na sake samun labari cewa wani daga cikin yan kungiyar,mai suna Shaibu (Sharpiro)ya dabawa yarona  ( Ndagi) wuka a daidai wajen wuyarsa.

Mallam Muhammed ya kara da cewa nan da nan shi da mahaifiyar yaron da sauran jama’ar gida suka bazama zuwa inda lamarin ya faru,amma kafin su kai wajen rai yayi halinsa. Yace marigayi Ndagi wanda bai jiba bai gani ba ya gamu da ajalinsa ne a yayin daya fita neman zufansa.

Sai dai kuma mahaifin marigayin wanda yace a matsayinsa na musulmi ya barwa Allah lamarin duk da hakan yayi kira ga mahukunta dasu rika daukan matakan hukunci mai tsananin akan duk wanda aka kama nan gaba ya aikata irin wannan danyen aiki.

“Ina mai bada shawarar aka dauki matakan kisa akan duk wanda ya kashe wani nan gaba don ya zama darasi ga wadanda suke aikata hakan nan gaba”inji Mallam Muhammed. Yace wannan shine karo na hudu ana rikicin kungiyoyin asiri na lakume rayukar matasa a unguwar, amma a cewarsa babu wani matakin da aka dauka na hukunta wadanda suka aikata laifin.

Da ya ke magana game da halayen dan nasa,wato marigayi Ndagi Idris Muhammed kuwa, Mallam Muhammed ya bayyana shi a matsayin yaro mai ladabi da biyyana da tarbiyya wanda ke bin umurnin iyaye da sauran jama’ar unguwa. Har ila yau ya bayyana shi a matsayin yaro mai mai jin kan iyaye kuma mai kwazo wajen neman na kansa.

Mahaifin marigayin wanda ya bayyana cewa ya kadu matuka gaya a yayin daya samu labarin rasuwar dansa(Ndagi) yayi addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya kuma sanya aljannah ya zama makomarsa.

Har ila yau wakilimmu ya samu tattaunawa da Mahaifiyar marigayi Ndagi, wato Malama Fatima Muhammed wanda tace har  ta bar duniya ba zata taba mantawa da wannan rana data rasa ran dan nata ba.

Ta ce, “na yi magana da shi ta waya bai kai minti biyar na samu labarin an soke shi da wuka.Kafin Kafin ni da mahaifinsa da sauran mutane mu kai wajen rai yayi halinsa. Sai dai kawai mu ka tsince shi cikin jini.”

Malama Fatima wanda ta barke da kuka yayin da wakilin namu ya ke zantawa da ita, ta ce sun barwa Allah lamarin a matsayinsu na Musulmi, sai dai tayi kira ga gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki dasu dauki matakan kawo karshen lamarin wanda tace idan ba a dauki mataki ba, to, wataran za a rika bin jama’a dakunansu, ana karkashe su.

Ta kuma bayyana marigayi Ndagi a matsayin yaro mai tausayin iyaye,, ga ladabi da biyayya, tana mai cewa lamari da ba zata manta a rayuwarta na duniya.

Mahaifiyar margayin ta kuma yi addu’ar Allah Ya jikan dan nata da rahama tare da basu karfin jure rashinsa.
Wakilin LEADERSHIP A YAU yayi kokarin zantawa da mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kogi, Mista Williams Ayah, akan lamarin, amma ya ci tura.

Rikicin yan kungiyar matsafa yana kara kamari a garin Lokoja da kuma sauran wurare a jihar Kogi.

Ko a kwanakin baya ma, sai da yan kungiyar matsafar suka hallaka wani dalibi dake karatu a jami’ar jihar Kogi dake Anyigba.

Exit mobile version