Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya bayyana cewa akan batun sake fasalin Najeriya dole ne arewa ta yi magana da murya daya domin kare muradun mutanan da ake wakilita.
Alhaji Aminu Bello Masari ya fadi haka ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar APC ta gudanar a gidan gwamnatn jihar Katsina, domin kowa ya bada tasa gudunmawa da za a tunkari wannan taro na jin ra’ayoyin jama’a akan gyara fasalin kudin tsarin mulkin Kasar nan.
Haka kuma gwaman ya ce wannan ba wai batu bane da mutun daya ba, abu ne da ya shafi al’umma, saboda haka ya zama wajibi kowa ya bada tasa gudunmuwa, indai dan asaliin Katsina ne, ba tare da nuna banbancin siyasa ba, magana ake ta kasa baki daya.
Haka kuma gwamnatin jihar Katsina ta kafa wani kwamitin da zai tuntubi wadanda suke da ruwa da tsaki a karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Katsina, Alhaji Sa’idu Barda da wasu manyan mutane na wannan jiha, domin su ka wo mutane da za su shi ga cikin wannan lamari.
Ya kara da cewa idan ana maganar tsarin mulki to ana maganar abin da ya shafi rayuwar mutane, dole akwai malaman addini, domin ya zuwa yanzu an fara samun ra’ayoyi ma bambanta da suka shafi addini inda wasu ke ganin ya kamata a canza tsarin mulkin a koma na asali.
Tun da farko a jawabinsa na maraba shugaban jam’iyyar APC a jihar katsina Malam Shitu S. Shitu ya bayyana cewa dalilin wannan taro shi ne domin a tattauna akan wannan mahimmin batu na gyara fasali tsarin mulkin kasa, sannan daga baya za su shiga wani batu da ya shafi jam’iyyar APC a jihar Katsina.
Shugaban Jam’iyyar ya kara da cewa tun farkon wannan tafiya babu wani hakki da ya shafi jam’iyya wanda gwamnatin jihar Katsina bata sauke ba, saboda haka yana ganin abin da kawai ya fi shi ne, su kara dinke barakar da ke tasowa.
Malam Shitu. S. Shitu ya shawarci mutanan Katsina da su tabbatar sun bada ta so gudunmawa wajan wannan batu mai matukar mahimmin, da ya shafi rayuwar mutanan arewa da Najeriya baki daya domin gudun kadda a bar arewa a baya.
Daga karshe an bada dama ga mahalarta taron su bayyana abin da suke ganin ya kamata ayin akan batun da ya shafi sauya fasalin Kasa da ake tunkara a halin yanzu.
Haka kuma taron ya samun halarta shugabanin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na jihar Katsina da ‘yan majalisar tarayya da na jaha da ‘yan kasuwa da kuma ‘yan kwangila, daga bisani kuma a rufe kofa domin ci gaba da tattaunawa akan abin da ya shafi jam’iyyar a matakin jiha, inda manema kabarai suka fita daga dakin taron.