Sauye-Sauye Da Ci Gaban Da Gidan Talibijin Na CCTV Ya Samu Cikin Shekar 60 Da Kafuwa

A ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2018 din nan ne babban gidan talabijin na kasar Sin wato CCTV, ya shirya bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwa, tare da fara watsa shirye shiryen talibijin, tun bayan kafa sabuwar kasar Sin.
Gidan Talabijin na CCTV, wanda aka kafa shi a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1958, ake kuma kiran sa da gidan talabijin na Beijing a wancan lokaci, yanzu haka yana da tashohi 50, yana kuma watsa shirye-shirye daban-daban da manyan yarukan duniya guda shida, inda sama da mutane biliyan guda ke kallonsa a sassan duniya daban daban.
Tun daga ranar 2 ga watan Satumbar shekarar 1958, CCTV ya fara watsa shirye-shirye wadanda galibinsu suka kunshi labarai, da shirye-shirye na musamman, da na ilimantarwa, da na ban dariya, da wasan kwaikwayo galibinsu salon na Opera. Wannan gidan talabijin ya samu sauye sauye da dama, tun bayan fara watsa shirye shiryensa kawo yanzu.
Domin gano dalilan nasarori da CCTV ya samu kawo yanzu, mu kalli tarihin gwagwarmayarsa, da kuma manyan sauye sauye da ya gudanar kawo yanzu.
Da fari CCTV ya fara watsa shirye shiryensa ne a ranar 2 ga watan Satumba na shekarar 1958 da tasha guda daya, amma sakamakon karuwar bukatar mabanbantan shirye shirye, sai aka samar da tasha ta biyu a shekarar 1963, kana tasha ta uku ta biyo baya a shekarar 1969.
Ba da jimawa ba kuma, a shekarar 1972 tashar ta fara yada shirye shiryen ta bai daya ta kafar tauraron dan Adam, bisa salon hotuna masu motsi launin fari da baki. Game da samar da hotuna masu motsi dake dauke da kaloli da dama kuwa, a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1973, gidan talibijin din da har a wancan lokaci ake kira da gidan talibijin na Beijing, ya fara nuna shirye shirye masu kala, a kan tashar sa ta biyu a matsayi na gwaji a duk ranekun Talata, da Alhamis, da kuma Asabar, ta hanyar amfani da fasahar PAL-D. Daga bisani kuma a shekarar 1977 ya fara gudanar da shirye shirye masu cikakkiyar kala baki daya.
Tarihi ba zai manta da ranar 1 a watan Mayun shekarar 1978 ba, ranar da gidan talabijin din ya sauya suna zuwa babban gidan talabijin na Sin, wato “China Central Television” ko CCTV a kaice.
Kawo karshen shekarun 1970, CCTV na watsa shirye shirye ne daga safiya zuwa maraice, sa’an nan a rufe tashoshinsa da tsakar dare. Har ila yau, a lokutan hutun ’yan makaranta na tsakiyar bazara da lokacin sanyi, da rana, yana gabatar da shirye shirye na musamman ga dalibai.
Ya zuwa shekarar 1985, CCTV ya riga ya zama gidan talabijin mafi girma, wanda shirye shiryensa ke karade dukkanin kasar Sin.
Da fari, sashen watsa bayanai na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulkin Sin ne ke ba da umarni, game da shirye shirye da gidan talabijin din zai rika yadawa. Amma bayan gudanar da sauye sauye a shekarun 1990, sai jam’iyyar kwamis ta samar da sabbin ka’idoji na gudanar da ayyuka ga CCTV. Wadannan ka’idoji sun kunshi damar “samar da shirye shirye bisa ikon tashar” da “karbuwar su bisa salon musamman na kasar Sin”, wanda hakan ya rage ikon da gwamnatin tsakiyar kasar ke da shi a kan gidan talabijin din.
CCTV ya ci gaba da samun tagomashi, inda a ranar 2 ga watan Satumbar shekarar 2008, yayin bikin cikarsa shekaru 50 da kafuwa, aka bude sabon katafaren ofishinsa. Kana a watan Yuli na shekarar 2009, CCTV ya kaddamar da tashar sa ta harshen Larabci.
Yayin da tashar CCTV ke cika shekaru 60 da kafuwa, ana iya cewa gidan talabajin din ya samu karin sauye sauye, da nasarori masu ban mamaki, ciki hadda sauyin matsayi da ya samu, inda a watan Maris na bana, ya tashi daga matsayin jigo guda a fannin watsa shirye shiryen talabijin, zuwa bangare na gungun kafofin watsa labarai na kasar Sin, karkashin babbar hukumar gidan rediyo da talibijin ta kasar Sin wato China Media Group ko CMG a takaice.
Ko da a baya bayan nan ma babbar hukumar gidan rediyo da talibijin ta kasar Sin wato CMG, ya ayyana shirinsa na bude sabon salon allon talibijin na zamani, mai dauke da fasahar 4K tun daga ranar 1 ga watan Oktoba, ta tashar CCTV4K. Bisa wannan ci gaba, birane 13 ciki har da Beijing, da Shanghai, da wasu biranen dake lardin Guangdong, a karo na farko, za su iya kallon shirye shirye ta akwatin talabijin din su, bisa fasahar 4K. Wannan fasaha a cewar masana, tana ba da damar kallon hotuna mafiya inganci, da sauti mafi kyau tamkar wadda ake samu a allon Sinima. Wannan na nufin ta tashar CCTV4K, masu kallo za su more shirye shiryen talabijin a gida, kamar suna cikin gidan Sinima.
Dukkanin wadannan sauye sauye, da ci gaba da gidan talabajin na CCTV ya samu, a iya cewa sakamako ne na jajircewa daga bangaren mahukuntan kasar Sin, wadanda ke dora muhimmancin gaske game da inganta sha’anin watsa shirye shirye ga al’ummar kasa, da ma sauran duniya baki daya.
Hakan ne ma ya sanya cikin sakonsa na taya murnar cikar CCTV shekaru 60 da kafuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya nuna farin cikinsa ga nasarorin da CCTV ya samu. Ya kuma gabatar da matukar yabo kan manyan nasarorin da aka cimma a fannin aikin talibijin a kasar, yana mai ba da tabbaci kan bunkasuwa, da nasarori da aka samu, kana ya bukaci da a bude sabon babi na aikin talibijin.
Shugaba Xi Jinping, ya bukaci da a kafa sabuwar kafar watsa labaru, wadda babu kamarta a duniya a fannin karfin jagoranci, da yada labaru, da kuma tasiri.
Rawar da take takawa ga ci gaban kasa
Sanin kowa ne a duniyar yau, kafofin watsa labarai na kan gaba wajen gabatar da bayanai iri daban daban, da suka hada da na wayar da kai, da nishadantarwa, da fadakarwa, da ma na gabatar wa al’ummun duniya halin da duniya ke ciki a yau.
Babbar gudummawar da za a ce CCTV ya bayar shi ne yayata manufofin gwamnatin kasa karkashin jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar. Kaza lika ya ba da gudummawa wajen sada Sinawa da labaran abubuwan dake faruwa a sassa daban daban na duniya. Tashoshin CCTV sun shahara wajen yada shirye shirye na irin ci gaban da kasar Sin ke samu.
Har wa yau akwai shirye shiryen wayar da kai game da harkokin kasuwanci da cinikayya, da na bunkasa al’adun kasa, da na wasanni. Sauran sun hada da shirye shirye kimiyya da fasaha, da raya tattalin arziki, da sauran su.
Domin tuna baya da hangen gaba, yanzu haka CCTV na gabatar da shirye shiryen tarihi, da ci gaban Sin da ma nahiyar Asiya. Baya ga haka tana gabatar da wasu karin shirye shiryen game da tafiye tafiye da harkokin sufuri, wadanda ke wayar da kan al’umma game da yanayi daban daban da ake samu a sassan kasar da mabanbantan al’adu na wurare daban daban.
A bangaren kasashen waje kuwa, CCTV na samar da shirye shirye game da nahiyar Afirka da Turai da sauran yankunan duniya. Hakan ne ma ya kai ga kaddamar da cibiyar Afirka, da aka kafa a ranar 11 ga watan Janairun shekarar 2012 a kasar Kenya. Wadda ke yada shirye shirye musamman domin Afirka. Hakan ya zama wani muhimmin mataki na karfafa hadin gwiwa da musayar al’adu, tare da yayata manufofin Sin da nahiyar Afirka ga al’ummun sassan biyu, da ma sauran kasashen duniya baki daya. (Marubuci: Saminu Hassan, ma’aikacin sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version