A baya bayan nan yayin taron MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya sanar da sabon burin Sin na samar da gudummawa kan sauyin yanayi a wani sabon zagaye. Kasar Sin ta dade tana daukar kwararan matakai kuma ingantattu, na tinkarar matsalar sauyin yanayi, inda ta zama kasa mafi cika alkawarinta na rage abubuwa masu gurbata muhalli.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da shugaban Amurka ya bayyana matsalar sauyin yanayi a matsayin “Damfara”, lamarin da ya bayyanawa duniya karara cewa, wasu kasashe suna kawai suke so da neman iko, ba tare da son daukar nauyi ba.
Duk wata babba, kamata ya yi ta zama abar misali ga sauran kasashe, kuma irin wannan dabi’a kasar Sin take nunawa. Matsalar sauyin yanayi matsala ce da ake ganin tasirinta yanzu haka, kuma ba ta bar kowa ba, har ma wadanda abun da suke fitarwa na hayaki mai gurbata muhalli bai taka kara ya karya ba.
Wannan sanarwar ta baya bayan nan da kasar Sin ta yi, ya samu yabo sosai, musammam daga sakatare janar na MDD, yana jaddada cewa, shirin na Sin na da muhimmanci matuka ga tunkarar sauyin yanayi. Su ma kafafen yada labarai na kasa da kasa da manyan jami’an hukumomi da kasashe da dama, sun yaba wa shirin, wanda ya nuna cewa, ana kara ammana da irin rawar da kasar Sin ke takawa a harkokin da suka shafi duniya.
Ba alkawari da gabatar da shirin kadai take yi ba, ta kasance mai aiwatar da su a aikace kuma ana ganin nasarorin da take samu a zahiri. Zuwa yanzu, babu wata kasa da ta bayar da gudunmuwa a wannan bangare kamar kasar Sin, kuma abun takaici shi ne, maimakon a dauki haka a matsayin zaburarwa, wasu na gujewa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Zuwa yanzu, kasar Sin ta zama jagora a fannin kirkirowa da amfani da makamashi mai tsafta. Ta kasance kasa mafi samar da kayayyakin sola a duniya, inda karfinta a bangaren ya zarce na duk duniya baki daya. Haka ma idan aka tabo karfin samar da lantarki daga iska da ruwa. Bugu da kari, tana kara cimma burinta na rage fitar da hayakin Carbon, inda daga 2005 zuwa 2020, yawan hayakin da take fitarwa ya ragu da kaso 48, kana tattalin arzikinta na habaka cikin sauri fiye da yawan hayakin da take fitarwa.
Kudurinta a wannan bangare ne ya sa take kai wa ga cika alkawuranta kafin ma lokacin da ta ayyana, wanda ke nuna da gaske take kuma ta amsa sunanta na babbar kasa mai sauke nauyi da ganin an samu duniya mai kyakkyawan muhallin rayuwa ga daukacin bil adama. (Fa’iza Mustapha)