‘Sawun Kura….’, Ta Wuce Kasa Ta Sha Zagi

Tare da Dakta Aliyu Ibrahim Kankara  07030797630

imel: ibrahim@fudutsima.edu.ng

 

Ranar Alhamis 28/12/2017 kasida ta ta fito a wannan jarida mai suna LEADERSHIP A Yau ta Hausa, mai taken ‘Wasu Fuskokin Makwabtaka a Kasar Hausa’ inda na nuna rashin jin  dadina da wani tsohon makwabcina da mu ka yi zama tare, wanda a sanadiyyar fadan ‘ya’yanmu ta sa ya biye ma matarsa har ya yi ta muzguna mani, na gaji na tashi na bar gidana din da ma unguwar baki daya. Wanda kafin wannan lokacin, idan aka ce mani makwabci za ya iya azalzala ta ya hanani zama gida na halaliya ta da na saya da kudi na har in tashi in bar masa gidan da ma unguwar wallahi summa tallahi zan yi gardama. Ga shi a cikin birnin Katsina makwabci ya fitine ni ya matsa ma rayuwa ta dole na tashi, ni da iyalina na bar masa unguwar na koma wani wuri daban na tsugunna. Duk in ka kewaya a cikin Duniya ba inda ake taka hakkin Dan Adam, a wulakanta shi sai a Duniyar Malam Bahaushe. Shi Bahaushe, shi ne ba gaira ba dalili za ya addabi makwabcinsa ya hana shi zama kusa da shi, ya Allah ko in ya ga ya fishi samun abin Duniya, ko ya fi shi sana’a mai kyau. Galiban, mutane ba su san hakkin makwabtaka ba. A sha’anin zamantakewa na makwabtaka, duk mutumin da ya biye ma matarsa ya rika daukar zancenta a kan fadan ‘ya‘yansa da na makwabta, to na tabbata har ga Allah ba za ya taba zama lafiya ba. Ita kuwa mace ta na da son zuciya, Allah Ya gina ta a kan son kanta. Magana ce ta gaskiya, mai wuyar fadi.

Bayan ma wannan, masu magana sun ce zomo ba ya fishi da makashinsa sai maratayinsa. Babban abin da ya bata mani rai har na sake yin yunkurin bitar labarin satin da ya gabata shi ne da wani mutum wanda bai bayyana mani sunansa ba ya aiko mani da sako a waya na nuna rashin jin dadinsa don na bayyana abin da ya dame ni, na wasu halayen na Bahaushe su na da bukatar gyara. Ya ce ban yi wa Bahaushe adalci ba in da har ya kamfato wani sashe na daga rubutu na: ‘….wannan shi ne kadan daga cikin halin Bahaushe mutumin Arewa wanda ya tashi cikin tsiya da talauci, na rashin darajar makwabci’. Sai kuma ya ce ma ni ‘karya ka ke yi wa Bahaushe’. To, a nan minene na fada? Abin da duk na fadi na yi karya ne? Ni dai na san duk tsiyarsa, komin tsiyarsa ba ya iya wanke Bahaushe ya nuna atafau ba ya da laifi a Duniya.

Kamar yanda ya turo sako: ‘tun zuwan Turawan Mulkin Mallaka sun iske Malam Bahaushe da ilimin addini da sana’o’I kala-kala, ga zumunci, ga kyauta ga tsarin shugabanci’. To, na kira shi da wannan lamba amma bai dauku way aba, na tura masa sako bai maido da amsa ba. Na kuma tura masa da lambar imel nawu, na yi masa bayani cewa ya turo da martani na abinda na rubuta, duk abin da za ya fadi ya fadi ko da zagina za ya yi ya zage ni ni kuma insha Allahu zan tura ma gidan jaridar su buga. Saboda mi na yi masa haka? Saboda adalci. Sabili da shi tunani da ilimi da fahimtar al’amurran rayuwa, kowa da irin nasa. Da da gaske yak e, da ya aiko mani da martani, ni kuma sai in tura masu su wallafa, ka ga a nan an karu. Ba na shakkar shi, ko wani ya kalubalance ni akan rubutu, idan na yi. Na wallafi littattafai 40 a rayuwata, kuma kowanne ya fuskanci kalubale. An sha yi mani tarnaki da tarki akan rubuce-rubuce na, kai har zagi na an sha yi amma ba ni damwa, saboda mutane manazarta kowa da yanda ya ke fahimtar rayuwa. Inda wannan malami ya bata mani rai da har yanzu bai maido mani da amsa ko martani ba. Kuma shi, ina mamakin wai ga ciwo a tare da shi amma bai san ya na da shi ba.

Ashe ya manta cewa ba ma tun kafin zuwan Turawa ba, tun zamanin jahiliyya kafin zuwan Musulunci aka san Malam Bahaushe da alkunya da kawaici da girmama naga ba da shi da neman na kansa, watau neman aiki ko sana’ar yi. Halayen Bahaushe abin koyi ne saboda ya na da tabi’o’I nagari masu kyau abin sha’awa. Shi ya sanya da musulunci ya zo Bahaushe bai sha wahala wajen karbarsa ba, kuma shi Bahaushe, shi ne ke aiwatar da addinin musulunci yanda ya zo, ba ya yi masa kwaskwarima. Wannan ya nuna cewa Bahaushe na da al’adu da tabi’o’I wadanda su ka yi kamanni da al’adun Larabawa. Duk kabilar da ke Duniya, babu wanda al’adarsa ta yi kama da ta Balarabe sai Bahaushe, shi ya sanya mu ka zauna lafiya. Ya kamata malamin da ya yi mani sakon bakar magana ya san wannan. Ni na fi shi sanin kowanene Bahaushe. Ko maguzawa da ba su da addinin musulunci su na da al’adu da tabi’o’I masu kyau, masu ban sha’awa. A da, maguzawa mat aba su zina. Mace ko wacece ita sai ta yi kokari ta kai bantenta, in ko ba haka ba ranar auren ta rannan bagiro ko Dodon su na tsafi za ya cinye ta. Wannan magana haka ta ke.

Daga baya ne Malam Bahaushe ya lalace ya zama malalaci. Ya zubar da tarbiyyarsa da al’adarsa ya dauko al’adun wasu al’umma marasa kunya ya yafa ma kansa. A da, ba a san Malam Bahaushe da karya ko munafunci ba, ba a san Bahaushe da gulma ko zaman banza ba aikin yi ko sana’a ba. A da, ba a san bahaushe da sata ko fashi da makami ba, tun daga kan ‘ya’yan riga (musulman) zuwa maguzawa. To don mi ya sanya a da in Bahaushe ya yi sata (lokacin da tarbiyyar mu ta fara tabarbarewa) sai ya bar garin su saboda kunya?

Wai yau an wayi gari su Malam Bahaushe su ne har da kwartanci ko neman matar aboki, su ne fashi da makami, su ne har da tsafi don neman kudi ko abin Duniya.

Malam mai aiko sako cikin fishi, in dai har da gaske ka ke, to ka maida martani ka aiko mani ko da zagina ne ka yi, don abin da z aka rubuta na tabbata za ya iya amfanar mai karatu, mai son sanin halayen Bahaushe. Don Allah kada ka mayar da ni sawun kura. Sawun kura shi ne, in ji Malam Bahaushe, ana jin tsoron mutum sai idan ya wuce a zage shi a bayansa ko keyarsa. Ka yi batu, na takale ka da Magana ka yi shiru. Kenan ka nuna kai matsoraci ne.

Marubuta littattafai da manazarta da kuma mawakan rubutattun wakokin Hausa sun sha yin bita da nazari akan halayyar Bahaushe da yanda ya koma malalaci. Musamman Malam Sa’adu Zungur, wanda ya ce muddin ba a daina zuwa gidan Magajiya ba, da yawan barace-barace a kan tituna, da tumasanci da maula, to Bahaushe ba za ya daina abin kunya. Duk Duniya ba mai bara da maula sai Malam Bahaushe. Kazalika duk Duniya ba mai maida abin da bai kai ya kawo ba bai isa a mayar da shi sana’a ba, abin sana’a sai Malam Bahaushe. Alal misali: yin zagi ko sana’ar bumburutun mai, ko roko. Dukansu ba su da nasaba da  addinimu da ma al’adarmu. Daga baya ne saboda lalacewa Bahaushe ya mayar da su sana’a. Akwai ma wasu sana’o’in na kaskanci kamar mutum ya nemi almajiri maras baki ya rike shi ya rika neman masa kudi, idan ya tara masa shi kuma ya amshi sallamarsa.

Ya kamata mu gyara.

 

Exit mobile version