Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ayau Juma’a, ta ce shirin Gwamnatin Tarayya na shirin sayar da kadarorinta zai amfani ’yan Niieriya kuma zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.
Ta bayyana hakan ne a yayin zantawarta da gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily, Ahmed, wacce kuma ita ce Ministar Kasafin Kudi da Tsare-Tsare ta Kasa, ta ce a yanzu haka wasu kadarorin gwamnati sun mutu kuma basu da kima ko daraja ko kadan ga ’yan Nijeriya a halin da suke ciki.
Ministan ta ce “Akwai wasu kadarorin gwamnati da suka mutu wadanda za a iya sayarwa kamfanoni masu zaman kansu don sake farfado da su don amfanin ‘yan Nijeriya.”
“Don haka muna duba daban-daban – kuma ni memba ce ta Majalisar Kula da sayar da kadarorin gwamnati – muna duba bangarori daban-daban na kadarorin gwamnati wadanda gwamnati ba ta iya sarrafawa, to ya dace a mika su ga kamfanoni masu zaman kansu.
A yau Juma’a, Ahmed ta jaddada cewa “niyyar ba wai kawai a samar da cikon kudin kasafin ba ne, akwai bukatar sake farfado da wadannan kadarorin tare da mika su ga kamfanoni masu zaman Kansu don bada gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin Kasa.”
Ta kara da cewa Ofishin ma’aikatun gwamnati zai fara hada kai da sauran bangarorin gwamnati kan siyar da kadarorin a farkon zangon shekarar.
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, kungiya mai kula da dukiyoyin gwamnati mai zaman kanta SERAP ta nemi Majalisar Dokoki ta kasa da ta dakatar da gwamnatin tarayya daga sayar da kadarorin jama’a don daukar nauyin kasafin kudin 2021.
Kungiyar ta ce, a maimakon haka, ya kamata gwamnati ta sake duba wasu fannoni a cikin kasafin kudin don rage yawan kudin kasafin, kamar rage yawan albashi da alawus-alawus ga jami’an gwamnati.