Abba Ibrahim Wada" />

Schweinsteiger Ya Yi Ritaya Daga Buga kwallon kafa

Tsohon dan kwallon tawagar Jamus da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da Bayern Munich, Bastian Schweinsteiger ya yi ritaya daga murza leda bayan ya shafe shekara da shekaru yana buga wasa a matakai daban daban.
dan wasan mai shekara 35 a duniya ya sanar da hakan ne kwana biyu bayan kammala gasar kwallon kafar Amurka ta Major League ta bana, inda kungiyarsa Chicago Fire ta kare a mataki na 17 a kasan teburi.
Schweinsteiger ya lashe kofin duniya a shekara ta 2014 wanda aka buga a kasar Brazil da kuma kofi takwas na gasar Bundesligar Jamus a Bayern Munich kuma dan wasan mai buga tsakiya, ya yi wa tawagar kwallon kafar Jamus wasanni 121 tsakanin shekara ta 2004 zuwa 2016.
Haka kuma ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Bayern wasanni 500, inda ya lashe gasar cin kofin zakarun turai na Champions League daga nan ne ya koma buga gasar firimiya a Manchster United.
Schweinsteiger wanda ya koma Manchester United a shekara ta 2005 ya yi wasanni 13 a shekara biyun da ya yi a Old Trafford, bayan da ya kasa taka rawar gani inda daga baya ne aka mai da dan wasan yin kwallo a cikin matasan Manchester United ‘yan shekara 23, daga baya Jose Mourinho ya ce ya yi da na sanin hukuncin da ya dauka.
Schweinsteiger ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chicago Fire a watan Maris din shekara ta 2017, ya kuma ci kwallo a wasan farko da ya yi wa kungiyar sai dai Chicago Fire ta kare kakar kwallon kafar Amurka a mataki na uku har ta buga wasannin cike gurbi a kakar farko ta Schweinsteiger, tun daga nan abubuwa suka yi ta lalacewa.

AC Milan Za Ta Kori Kociyanta

kungiyar kwallon kafa ta AC Milan na shirin raba gari da kocinta Marco Giampaolo, bayan da kungiyar ke tafiyar hawainiya a kakar bana in ji wasu rahotanni daga kasar Italiya da a ka wallafa ranar Talata
AC Milan tana tana mataki na 13 a kasan teburin Siriya A maki uku ne ya rage mata tsakaninta da ‘yan kasan teburi da za su iya barin wasannin bana kuma hakan ne yaja hankalin shugabannin kungiyar.
Giampaolo mai shekara 52, ya maye gurbin Gennaro Gattuso a bana sai dai kawo yanzu ya sha kashi a wasanni hudu daga cikin wasanni bakwai da ya ja ragama har da rashin nasara da ci 2-0 da abokiyar hamayya Inter Milan ta yi ma ta.
Milan ta yi rashin nasara a karawar da ta yi da kungiyoyin Torino da kuma Fiorentina, amma ta doke kungiyar kwallon kafa ta Genoa da ci 2-1 a karshen mako wanda hakan yasa kociyan yasamu kwanciyar hankali ta ‘yan kwanaki.
Kamar yadda manyan jaridun da suke wallafa labarai daga kasar Italiya suka wallafa, Luciano Spalletti ne zai maye gurbin Giampaolo, wato tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Roma da Inter Milan.
Ana kuma cewa watakila tsohon kocin Inter Milan da Fiorentina, Stefano Pioli ko kuma wanda ya horas da Roma da Marseille, Rudi Garcia daya daga cikinsu ya karbi aikin na koyar da kungiyar mai tarihi a duniya.

Har Yanzu Gareth Bale Na Cikin Takura A Real Madrid

Wani dan jarida daga kasar Sipaniya, Guillem Balague, ya yi ikirarin cewa dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Gareth Bale ya fusata sosai da kungiyar kuma ya na matukar son barin su.
An yi tsammani Bale zai sanya hannu kan kwantaragin shekara uku da kungiyar Jiangsu Suning da ke buga gasar lig-lig a kasar Sin wato China a bazara inda za a biya shi fam miliyan daya a kowane mako amma Real Madrid sun ki amincewa da hakan domin suna so a ba su kudin barin kungiyar, wato (transfer fee) a turance.
A watan Yuli, kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce suna fata Bale zai bar kungiyar nan ba da dadewa ba, abin da ya sa wakilin Bale, Jonathan Barnett ya mayar da martani cewa Zidane abin kunya ne ba ya martaba dan wasan wanda ya yi aiki tukuru a Real Madrid.
Bale ya lashe kofin Zakarun Turai guda hudu da na La Liga daya da gasar cin kofin Copa del Rey da na Uefa uku da kuma gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi a Real Madrid inda ya zura kwallaye fiye da 100 tun bayan zuwansa kungiyar.
Bayan an hana shi komawa kasar China, dan wasan mai sh

Exit mobile version