Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya aza tubulin ginin wasu manyan hanyoyi guda biyu a karkashin shirin fafada fadar jihar Bauchi.
Har-ila-yau, shi ma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da wasu ayyukan hanyoyin guda biyu dukka a cikin kwaryar garin Bauchi wanda gwamnatin jihar ta bada su.
Hanyoyin sun hada da maida babban hanyar da ta taso daga titin Awala zuwa filin sauka da tashi na jiragen kasa da kasa da ke Bauchi tare da maida shi daga layi daya zuwa tagwayen hanyoyi; sai kuma maida hanyar da ya tashi daga Awalah zuwa jami’ar jihar Bauchi da ke kan titin zuwa Maiduguri zuwa tagwayen hanyoyi daga hanya mai layi daya; da kuma hanyar Dogon Yaro zuwa Zarandan Otel gami kuma da hanyar da ta tashi daga gidan man Mobile ya nausa zuwa mahadalar ofishin ‘yan kwana-kwana da ke jihar.
Dukkanin ayyukan sun kai kilomita 26 da aka bada kudinsu a kan kwangila naira biliyan 12. Wadannan ayyukan dai gwamnan jihar ta Bauchi Bala Muhammad ne zai gudanar da su a bisa muradinsa na sabuntawa da inganta jihar Bauchi.
Uche ya shaida cewar ba su yi mamakin namijin kokarin da gwamnan ke yi a Bauchi ba, muddin aka yi la’akari da irin himma da kwazon da ya nuna a lokacin da yake Ministan babban birnin tarayya Abuja, ya nuna kwarin guiwarsa na cewa tabbas al’ummar Bauchi za su mori gwamnatin Bala sosai.
Secondus ya tabbatar da cewar da zarar aka kammala wadannan ayyukan za su kai ga bunkasa tattalin arzikin jihar, inganta hanyoyin yawon bude ido da shakatawa musamman domin kara samar da maziyarta zuwa gandun dujin Yankari mai dumbin tarihi tare da wasu tulin alfanu da hanyoyin za su samar wa jihar.
Shi kuma a jawabinsa, gwamnan jihar Bala Muhammad, ya nuna cewa sun yi nazarin cewa jihar tana gayar bukatar muhimman ayyukan da za su fadadata tare da inganta jihar.
Ya shaida cewar nan da shekaru biyu ake son kammala wadannan ayyukan da aka kaddamar da su, baya ga wadannan, ya shaida cewar akwai muhimman ayyukan gina titina da gadaje da yanzu haka gwamnatinsa take kai da kuma wadanda ta samu nasarar kammalasu tun lokacin da ta zo kan mulki.
Ya kuma ce, za su cigaba da gudanar da ayyukan da za su kyautata jihar, inda ya gode wa majalisar dokokin jihar a bisa hadin kai da goyon bayan da suke ba shi a kowani lokaci wajen tabbatar da aiwatar da ayyukan da suka dace.
Shi ma da ya ke tofa albarkacin bakinsa, gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, ya misalta hanyoyin da aka kaddamar da fara yinsu a matsayin hanyoyi da za su kara wa jihar Bauchi tagomashin samun ababen more rayuwa da daman gaske, tare da bunkasa harkokin kasuwanci.
Ya ce, samar da hanyoyi masu nagarta na kara sada jama’a da jama’a wanda kuma ake riskar dumbin ababen more rayuwa matuka gaya.