Connect with us

LABARAI

Secondus Ya Taya Oshiomhole Murnar Zama Shugaban APC

Published

on

Shugaban Jam’iyyar adawa ta PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya taya tsohon gwamnan jihar Edo Kwamared Adams Oshiomhole murnar zabensa da aka yi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Prince Secondus ya aike da taya murnar tasa ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Kakakinsa Aide Ike Abonyi ya sanya wa hanu, ya yi fatan alkairi wa Adams kan wannan kujerar da ya samu.
Haka kuma, ya bukaci shugaban APC da ya tabbatar da wanzar da demokradiyya a fadin kasar nan.
Sanarwar ta ce; “A madadin jam’iyyata, babbar jam’iyyar adawa a kasar nan wato PDP, ina taya murna da kuma fatan wanzar da demokradiyya a yayin da yake ofis a matsayin shugaban APC ta kasa,” Inji shugaban PDP.

Advertisement

labarai