Rabiu Ali Indabawa" />

Senegal Ta Daure Sall Shekara Biyar A Gidan Yari

Wata kotu a Senegal ta yanke wa daya daga cikin fitattun ‘yan siyasar kasar, Khalifa Sall hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari saboda samunsa da laifin almundahana. Masu sa ido a siyasar kasar na kallon matakin a matsayin wani yunkuri na hana shi kalubalantar shugaba Macky Sall a zaben shekarar 2019.

Kotun ta ce, ta samu Khalifa Sall wanda ya rike mukamin Magajin Garin Birnin Dakar da laifin amfani da kudaden gwamnati ta hanyar da ba ta kamata ba, abin da ya sa aka daure shi shekara 5 a gidan yari da kuma cin tarar sa Sefa miliyan 5 ko kuma Euro dubu 7da 625. Kotun ta ce, ta gamsu da shaidun da aka gabatar ma ta wadanda suka hada da cin amana da halarta kudaden haramun da kuma ruf da ciki da kudaden talakawa.

Masu gabatar da kara sun bukaci a daure Sall shekaru 7 a gidan yari da kuma cin sa tarar Dala miliyan 10, amma sai alkalin kotun ya amince da daurin shekaru 5.

Lauyan dan siyasar, Cheikh Khouraissi Ba ya ce, zai daukaka kara domin kalubalanatar hukuncin a shari’ar da ta dauke al’ummar kasar hankali saboda farin jinin da dan siyasar ke da shi.

Magoya bayan Sall da suka cika kotun sun yi ta bayyana rashin amincewarsu da hukuncin.

 

Exit mobile version