Connect with us

RIGAR 'YANCI

SERAP Ta Maka Gwamnatin Nijeriya Kotu Kan Raba Kayan Tallafin Korona

Published

on

Kungiyar kare hakkin tattalin arziki ta SERAP ta maka gwamnatin tarayya a gaban babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, inda take neman bayanin gwamnatin tarayyan da babban bankin Nijeriya a kan raba kayayyakin tallafin Korona a cikin kasar nan.

kungiyar ta nemi kotun da ta umurci gwamnatin tarayyan da kuma babban bankin da su bayyana sunan duk wani dan Nijeriyan da ya amfana da tsarin raba kudin tallafi da kuma yanda aka yi rabon kayayyakin abinci da sauran kayan tallafi a lokacin dokar kulle a Abuja da Legos da Ogun a sanadiyar annobar ta Korona.

Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi kungiyar ta SERAP ta ce shigar da karar ta biyo bayan bukatar neman bayani ne da take da hakki a kansa wanda ta aike a ranar 4 ga watan Afrilu, 2020, inda take bayyana koken milyoyin ‘yan Nijeriya matalauta da marasa galihu da sam ba su amfana da komai ba daga duk ababen tallafi, gudummawa da ake yayata cewa an rarraba.

karar da kungiyar ta shigar mai lamba, FHC/ABJ/CS/657/2020 wacce Lauyoyin kungiyar, Kolawole Oluwadare da Joke Fekumo, suka shigar a makon da ya gabata tana cewa ne, “A bisa hakkin doka mai lamba FoI da kuma hakkin mutuntaka ta Afrika, muna bukatar a umurci Malama Umar Farouk da Mista Emefiele, a kuma tilasta masu da su bai wa al’umma bayani dalla-dalla a kan ko su waye suka amfana da kayayyakin tallafi da sauran gudummawar da aka tara a lokacin annobar Korona.

“Duk wani bayani da zai nuna cewa kayayyakin tallafin, gudummawa da sauran taimakon da aka tara ba su iya kaiwa ga wadanda ya kamata su amfana da shi ba, hakan zai iya nuna rashin amana da gaskiyan shirin ne bakidayansa, da kuma hanyar da aka bi wajen rarraba kayan tallafin ga ‘yan Nijeriya.

“Kowane guda daga cikin Ministan ayyukan jinkai, annoba da sauransu da kuma Gwamnan babban bankin Nijeriya suna da hakki na shari’a a kansu da su bai wa hukumar SERAP bayani dalla-dalla a kan ko su waye suka amfana ya zuwa yanzun da kayayyakin tallafin na korona da aka rarraba, ko kuma su wallafa hakan a kafafen yada labarai kamar yanda muka nema da su yi wanda kuma har yanzun sun yi biris da bukatar hakan.

Kotun dai ba ta sanya wata ran aba domin fara sauraron shari’ar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: