Abba Ibrahim Wada" />

Serena Williams Da Kerber Za Su Fafata A Wasan Karshe Na Wimbledon

Gwarzuwar ‘yar wasan kwallon Tennis, Serena Williams, za ta kara da Angelikue Kerber ta Jamus a gasar Wimbledon ta mutum dai-dai bayan zaratan biyu sun tsallaka zuwa matakin wasan karshe na wannan gasa.
Williams Ba’amurikiya da ta kasance lamba ta daya a duniyar kwallon tennis a can baya, ta casa Julia Gorges ta Jamus da ci 6-2 da 6-4, yayin da Kerber ta casa Jelena Ostapenko ta Latbia da ci 6-3 da kuma 6-3.
A yau ne zaratan biyu za su kece raini da juna, wasan da ake kallo tamkar maimaicin fafatawar da suka yi da juna a irin wannan mataki a shekarar 2016, in da Serena Williams ta yi nasara.
A karo na 24 kenan da Williams ke neman lashe kambu a manya-manyan gasar Tennis wato Grand Slam, amma a karon farko kenan tun bayan da ta haihu

Exit mobile version