Sergio Romero Ya Koma Italiya Da Taka Leda

Romero

Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Sergio Romero ya koma Benezia ta kasar Italiya, bayan da kwantiraginsa ya kare a Old Trafford a karshen watan Yuli. Romero mai shekara 34 wanda yarjejeniyarsa ta kare a karshen watan Yuli, ya yi kakar wasa shida a Manchester United a matakin mataimakin Dabid de Gea dan asalin kasar Spaniya wanda ya shafe sama da shekara goma yana buga wasa a United din.

 

Wasa na karshe da dan kasar Argentina ya yi wa Manchester United shi ne na dab da na karshe a gasar Europa League da Copenhagen cikin Agustan 2020, wanda kungiyar ta Old Trafford ta yi nasara da ci 1-0. Shi ne mai tsaron ragar Argentina da ya dade yana buga mata wasa a tarihi inda ya buga wasanni 96 kawo yanzu kuma Romero wanda ya taimaka wa United ta lashe Europa a shekarar 2017, ya koma a matakin mai jiran ko-ta-kwana karkashin mai koyarwa, Ole Gunnar Solskjaer.

 

Sai dai Solskjaer ya mai da hankali ga Dean Henderson wanda ya koma United daga wasannin aro da ya tsare ragar Sheffield United a 2020, sannan Romero, wanda ya ci FA Cup da kuma EFL Cup a United, ya tsare ragar kungiyar sau 39 kwallon ba ta shiga ragarsa ba a wasanni 61 da ya yi mata sai dai Benezia tana mataki na 17 a kasan teburin Serie A na bana, mai maki biyar daga fafatawa bakwai a babbar gasar Italiya.

 

 

Exit mobile version