SGF Ya Bukaci Gudummawar Sarakuna Kan Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi

Sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya (SGF) Boss Gida Mustapha ya bukaci Sarakunan gargajiya da su yi amfani da kujerunsu wajen dabbaka zaman lafiya da yaki da shan miyagun kwayoyi a tsakanin al’ummominsu.
Boss Gida ya yi bayanin cewar idan sarakuna suka bayar da tasu gudummawar wajen ganin an rage yawaitar matsalar shaye-shaye hakan zai kawo ci gaba gaya wajen rage aukuwar matsalar tabarbarewar tarbiyya a tsakanin al’ummominsu.
Ya yi wannan kiran ne a jiya a cikin birnin tarayya Abuja sa’ilin da ya marabci tawagar kungiyar sarakuna ta kasar Nijeriya wato ‘National Council of Traditional Rulers of Nigeria (NCTRN)’ a ofishinsa.
Kamar yadda yake bayani, dabbaka zaman lafiya zai samu ne da hadin gwiwar sarakuna da gwamnati da rassanta gami da kungiyoyin da abin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kowane lokaci, yana mai bayanin cewar idan babu zaman lafiya babu wani ci gaban da za iya samu a cikin al’umma.
Etsu Nupe, Dakta Yahaya Abubakar shi ne ya jagoranci tawagar (NCTRN) mai mutane shida zuwa wannan ziyarar, wanda ya bayyana wa Sakataren gwamnatin cewar kungiyarsu za ta ci gaba da bayar da gudummawa wajen kyautata zaman lafiya da ci gaban kasar nan, sannan kuma ya ce za su ci gaba da tabbatar da ana kiyaye al’adun kabilu mabambanta domin wanzar da zaman lafiya don kyautata rayuwar ‘yan kasa.
Ya kuma shaida masa cewar tabbas sarakuna suna da ta cewa dangane da kara fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya da alhairan da ke cikin hakan, don haka ne ya ba shi tabbacin za su kara azama kan wanda suke yi domin kyautata kasar Nijeriya.

Exit mobile version