Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Sha’awar Karatu Da Rubutu Ta Sani Fara Rubuta Littafi

by
3 years ago
in Uncategorized
5 min read
Sha’awar Karatu Da Rubutu Ta Sani Fara Rubuta Littafi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Kamar  yadda masu karatunmu suka sani, wannan shafi ne da muke zakulo muku makaranta da marubuta litattafan Hausan don jin ta bakinsu game da abin da ya shafi karatun ko kuma rubutun. A  wannan makon mutattauna ne da marubuciyar littafin “Masakina”,  Asiya Abdullahi Yusuf. Masu karatu ku biyo mu don jin yadda muka tattauna da bakuwar ta mu ta wannan makon:

Ya sunan Malamar?

Sunana Asiya Abdullahi Yusuf, wanda aka fi sani na da shi kuma shi ne See-See.

Labarai Masu Nasaba

Har Yanzu Messi Ya Fi Kowa Daukar Albashi A Tamaula

Dakarun MNJTF Sun Yi Barin Wuta Kan ‘Yan Boko Haram Sun Kashe 300 A Tafkin Chadi

 

Masu karatu za su so su ji  dan takaitaccen tarihinki?

Farko dai ni haifaffiyar garin Katsina ce, kuma a nan na yi makaranta ta daga firamare zuwa sakandire, kuma har yanzu a cikinta nake rayuwa. A bangaren addini ma Alhamdulillahi shi ma na yi, domin har sauka na yi, kuma na karanta manyan littattafai daidai gwargwado.

 

Me ya ja hankalinki kika fada harkar rubuce-rubuce?

Abin kawai yana ba ni sha’awa ne da dade wa, sai na nuna wa wata marubuciya sha’awata a kan hakan domin ita ma ina karanta littafinta a wannan lokacin,  saboda haka, sai ta ba ni goyon baya sosai,  daga nan na soma har zuwa yau da muke wannan tattaunawa.

 

Wace hanya kika bi wajen ganin kin fara rubutu?

Na fara ne ta hanyar kafar sadarwa ta zamani.

 

In na fahimce ki kina so ki ce kin fara rubutu a online ne, shin kin taba buga littafinki?

Kwarai da gaske, ban taba ba har yau.

 

Wanne littafi kika fara rubuta wa?

Littafin da na fara rubuta was hi ne “Da Kai Kadai Na Dace”.

 

Me littafin yake kunshe da shi, wanne sako yake isarwa?

Illar cin amana, da kuma mahimmancin tsaya wa gaskiya duk inda ta je ta dawo.

 

Ya karbuwar littafin ya kasance a wajen makaranta?

Gaskiya Alhamdulillahi, na gode wa Allah domin littafin ya karbo a wajen makaranta, domin har gobe da bazarsu nake rawa har i zuwa ga sauran littattafaina.

 

Na wa ne adadin littattafanki?

Guda biyar, sai na shidda da yake yawo yanzu ma’ana nake kansa a yanzu.

 

Kamar wanne da wanne ke nan? Dan makaranta su gane littattafan.

Da Kai Kadai Na Dace, Soyayyar Gaskiya, Dalilin Yin Kuka nah, Masaki na, sai na yanzu Ba mu Dace Da Juna Ba.

 

Cikin  wadaannan littattafan naki wanne littafi ne ya fi baki wahala wajen rubuta wa, kuma wanne abu ne ya fi ba ki wahala a ciki?

Da Kai Kadai Na Dace, domin a lokacin sabuwar marubuciya za a kira ni, sannan ka’idojin rubutu sun ba ni wahala sosai domin na dade ban rike su ba.

 

Ko za ki iya fada wa masu karatu me littafin yake kunshe da shi ?

Abin da littafin yake kunshe da shi shi ne, labarin wasu kawaye ne guda biyu inda daya ta zama maciya amana, kuma tai amfani da damarta ta mace ta janye hankalin saurayin kawartata, amma duk daga karshe saboda ba zaman gaskiya suka yi ba zama ne na soyayyar mint kamar yadda ‘yan mata suke fada sai gashi daga karshe sun yi rabuwa marar dadi ita kuma Allah ya masanya mata da wani wanda ta dace da shi, wanda har a karshe ta kira shi da shi kadai ta dace.

 

Ya karbuwar littafin ya kasance ga su makarantan?

Gaskiya ya karbu sosai, domin masoyansa su ne har yanzu muke tafiya da su ga sauran littattafai na.

 

Idan aka ce ki zabi daya daga cikin littattafanki shin wanne za ki zaba kuma me ya sa kika zabe shi?

Da Kai Kadai Na Dace zan zaba, dalili kuwa shi ne, labarin kusan a kaina ya faru sannan na yi amfani da sunana ne da kuma sunan habibina.

 

Kina so ki ce labarin gaskiya ne ba kirkirarren labari ba ne?

Kusan gaskiya ne ba gaskiya ba, ma’ana a nan shi ne farkon labarin gaskiya ne sai dai a karshe na saka ita waccen ta yi aure ni kuma a gaskiyar labarin ban yi aure ba.

 

Gaskia ne, kin ma amsan tambayar da nake son yi miki don na san masu karatu suna ta kokwanto kan cewa wai shin kin yi aure ko kuwa ba ki ba? Toh mu je ga tambayar gaba, za ki kamar shekara nawa kina rubutu?

Daya da rabi koma biyu, domin zan iya rike na fara rubutu ne a 2017 farko farko sai dai ba na iya cewa ga watan.

 

Shin kin taba fuskantar wani kalubale cikin harkar rubutunki wanda ba za ki taba manta wa da shi ba?

A’a gaskiya, har zuwa yau ban taba fuskantar wani babban kalubale ba.

 

Ya batun iyaye fa? Shin sun amince da rubutun naki ko kuwa kina yi ne ba tare da sun sani ba? Kin san wasu iyayen suna ganin kamar bata tarbiyya ne ba sa barin yaran nasu su tsunduma cikin har kar shin ya abun yake ga naki iyayen?

A’a babu wata matsala, sai dai gaskiya ba na yin typing sai na tabbatar na kammala komai zan yi na aikina na gida ne ko kuma sauransu.

 

Makaranta da da ma suna koka wa ga marubuta kan suna wulakanta su yayin da suke bibiyarsu shin ya abin yake?  zancen gaskiya ne ko kuwa kage ne kawai ake wa marubutan?

Gaskiya magana hakan abin yake sai dai kinsan muna da yawa kuma ba za a taru a zama daya ba.

 

A yanzu wasu daga cikin marubuta littafin hausa na online sun maida littattafan su na kudi shin kema naki littafin kin maida shi ne ko kuwa har yanzu makaranta naci gaba da karantawa a haka ba tare da ko sisi ba?

A’a gaskiya har yau na kyauta ne, kuma banajin akwai ranar da zan mayar dashi na kudi insha Allahu

 

Wacce marubuciya ce ko marubuci ne ya fi burge ki a harkar rubuce-rubuce?

Wani marubuci da ya rubuta wani littafi Aljanna Fatima.

 

In na fahimce ki kina so ki ce Kingboi Isah ke nan, me ya sa rubutunsa yake burge ki?

Kwarai shi ne, Saboda littafinsa na Aljana Fatima domin labarin ya burge ni kuma ya ba ni dariya sosai.

 

Mene ne burinki na karshe game da rubutunki?

Ina da burin naci gaba da rubutuna kamar yanda nake a yanzu, cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fitina ba ko ka ce na ce a kaina.

 

Wacce shawara kike da ita ga marubuta har ma da makaranta?

Marubuta mu daina wulakanta masoyanmu domin da ba zarsu muke rawa, yau suna ja da baya ta ta mu ta kare, sannan abu na biyu don Allah mu daina saka maganganu mararsa dadi a cikin littattafanmu domin kada mu manta komai hakan ya jawo muma munada kaso a ciki. Makaranta kuma su dinga mana uzuri ba komai ba ne abin magana idan mun yi kuskure, domin muma ‘yan’adam ne kamar kowa, na biyu kuma don Allah su daina ba wa marubuta masu saka batsa a cikin littattafansu goyon baya a kan suci gaba domin wallahi hakan yana da illah sosai musamman tunda abin nan ba matan aure kadai suke karanta shi ba har da yara ‘yan shekara goma sha wadanda suke gabar balagarsu.

 

Allah ya sa sun ji, me za ki ce game da wannan shafi na Duniyar Marubuta da makaranta?

Amin. Gaskiya Alhamdulillahi shafin ya yi domin a ganina shi ma yana da na sa tasirin kuma ina addu’ar Allah ya daga shafin da ke kanki mai shi.

 

Amin, ko kina da wadanda za ki gaisar?

Kwarai, farko akwai Action Baby da Neenah cool, da A’ishan Umma sai BK, sai Raheenat, da Aunty A’isha Yola, Maryam Tijjani Adam, Nana Hauwa’u, Haliloss, Hafsy, da ke kanki Muhiebert Indiya da kuma sauran masoyana da ba na iya fadarsu saboda yawan su.

 

Muna godia sosai, ki huta lafiya, nan muka kawo karshen tattaunawarmu da marubuciyar wadda aka fi sani da See-See,

 

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Amfanin Lalle Da Kuma Magunnan Da Yake Yi

Next Post

2019: WaterAid Ta Shirya Muhawara Tsakanin Jam’iyyu Kan Sha’anin Ruwa Da Muhalli A Bauchi

Labarai Masu Nasaba

Messi

Har Yanzu Messi Ya Fi Kowa Daukar Albashi A Tamaula

by Abba Ibrahim Wada
1 day ago
0

...

An Yi Lugudan Wuta Ta Jiragen Yaki Kan Isis An Kashe Kwamandanta Bin-umar A Tabkin Chadi

Dakarun MNJTF Sun Yi Barin Wuta Kan ‘Yan Boko Haram Sun Kashe 300 A Tafkin Chadi

by Leadership Hausa
5 days ago
0

...

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

...

Ramadan: Diyar Marigayi Sheikh Ja’afar Ta Fara Tafsirin Al-qur’ani A Masallacinsa Da Ke Kano

An Kashe Mutum 172, An Yi Garkuwa Da 23 A Arewa Maso Gabashin Nijeriya Cikin Watanni 3 —Rahoto

by Leadership Hausa
1 week ago
0

...

Next Post
2019: WaterAid Ta Shirya Muhawara Tsakanin Jam’iyyu Kan Sha’anin Ruwa Da Muhalli A Bauchi

2019: WaterAid Ta Shirya Muhawara Tsakanin Jam’iyyu Kan Sha’anin Ruwa Da Muhalli A Bauchi

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: