Shafin kafar sadarwa na Facebook zai cire duk wata tala da za ta iya jawo nuna kyama ga Yahudawa, an ce akwai talla masu yawa da suke nuna kyama ga Yahudu a shafin, don haka za a duba a cire duk wani abu makamancin wannan.
Facebook sun ce suna kokarin cire duk wani abu da zai nuna alamar kyama ga wata al’umma, amma an fara da na nuna kyamar Yahudu ne don shi yafi yawa a shafin, sun ce akwai shiri da su ke da shi na ladabtar da masu nuna kyama, duk da wasu lokutan kalaman nuna kyamar suna yawan fitowa a shafin ba tare da sun ankara ba.