Shafin Twitter Zai Dau Mataki Kan Cin Zarafi

Daga Bakir Muhammad

Shafin sada zumunta na twitter na shirin daukar mataki akan duk abubuwan da suke nuna batsa da cin zarafin wani ko wasu, domin magance matsalolin da ma su tahamulli da shafin suke yawan korafi akai, za su gyara yanayin yadda suke duba korafin masu tahamulli da shafin ma, ta yadda za su dinda la’akari da korafe-korafe akan lokaci.

Shugaban shafin na Twitter Jack Dorsey ya ce lallai suna shirin daukar tsatsauran mataki kan masu cin zarafi a shafin, a ranar Juma’ar da ta gabata ne aka soki shafin na twitter bayan ya toshe akant din wata ‘yar wasan fim mai suna Rose Mcgown bayan ta zargi wani mai shirya fina-finai Harbey Weinstein da zargin yi mata fyade.

Shi dai Harbey Weinstein ya musanta duk zargin da Rose ta mishi, gwamnatin Birtaniya ma ta bukaci shafin a kwanakin baya da ya duba yadda zai magance matsalar cin zarafi da sauran matsaloli, ya shawarci kamfanin da ya sa kaimi matuka wajen magance matsalolin,

Kamfanin ya tabbatar da ya na kokarin ganin ya dauki matakin kan wadannan matsalolin da suka dade suna ci mishi tuwo a kwarya, sannan zai sanya sabbin dokoki da za su magance irin wadannan matsaloli a nan gaba, kamfanin yana shawara da masana daga kungiyoyi irinsu Safety Council don ganin yadda za su biyo ma al’ammarin.

Sannan za su fitar da dokokin da zasu magance matsalar masu akant da suke amfani da kalmomin tashin hankali wajen isar da sakon su, da ma wadanda suka taba tura wani sako da yake nuna fitina ko tashin hankali, ko da basu ne da kansu suka aika sakon ba, dukkan wadannan akwai mataki mai tsauri da za’a sanar a kansu.

Kamfanin ya tabbatar da zai canja yadda yake mu’amala da korafin masu amfani da shafin, zai dinga yin hakan cikin kankanin lokaci duk da bai yi karin bayani akan ya zai dinga yin hakan ba, tuni dai kungiyoyin kare hakkin mata suka fara yabon wannan mataki da shafin Twitter ke shirin dauka, wadanda a baya suke ganin shafin ya tauye wa mata ‘yanci.

Masana da dama suna ganin lallai wannan matakin zai magance matsalolin cin zarafi da suka yawaita a shafin, kuma suna ganin sam bai dace ace sakonnin cin zarafi sun wuce tsawon awowi 24 ba tare da an cire su ba, don haka suna ganin ya kamata duk sakon cin zarafi a cire shi cikin awowi 24, kuma dole shafin ya yi kokarin ganin hakan ya yiwu.

 

Exit mobile version