Shaguben Da Ghali Na’abba Ya Yi A Kan Shugabancin Nijeriya A Yanzu

Dimukradiyya

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Tsohon Kakakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na’Abba, ya bayyana cewa babu shugabanci a Nijeriya. Ghali Umar Na’abba, ya koka ne a kan yawaitar kashe-kashe da tashe-tashen hankula a kasar nan.

Kalaman na Ghali, wani shagube ne kan yadda Shugaba Muhammadu Buhari, ya kasa tsayar da kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasar nan. “Mafi lalacewa a cikinmu ne aka dauki amanar jagorancin al’ummar kasar nan aka damka a hannunsa.”

Ya yi wadannan kakkausan kalaman a wani taron da ya hada kan kabilun Nijeriya daban-daban a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Mahalarta taron sun hada da Ayo Adebanjo na Afenifere, Chukwuemeka Ezeife na Ohaneze-Ndigbo da sauran su.

Ghali ya yi kalaman ne a lokacin da Buhari ya cika shekaru shida a kan mulki, ba tare da magance matsalar tsaro da ya rika kamfen zai magance ba idan ya hau mulki. Kawar da matsalar tsaro na daga cikin manyan alkawuran da Buhari ya dauka tun kafin ya hau mulki.

‘Yan Nijeriya musamman ‘yan Arewa sun yi guguwar Buhari ne a 2015 domin ya magance matsalar tsaro da yankin ke fama da shi a wancan lokaci wanda ita ce matsalar hare-haren Boko Haram. Sai dai kuma shekaru shida bayan haka, maimakon a samu sauki, matsalar tsaro tsanani ya kara yi musamman a yanzu kuma a yankin Arewa Maso Yamma da Kudancin Nijeria.

Exit mobile version