Shagunan Siyayya Ta Shafin Intanet

Tare da Baƙir Muhammad

A yanzu a duniya shagunan siyayya na shafin intanet (Online Stores) su ake yayi , sun shahahara sosai a duniya, akwai manyan shagunan siyayya da suke siyar da ko wanne irin kayan siyayya in dai ba haramtattun kaya bane, misali akwai waɗanda suka fi shahara irinsu kamfanin Amazon, Ebay, Walmart, Alibaba da sauransu, kusan duk abinda kake buƙata na daga kayan wuta, kayan sawa, littafai, kai harda na’urori, manyan injina da ababen hawa kamar babur, keke da mota zaka iya samu a waɗannan shagunan na shafin intanet.

Tsarin siyayya a shagunan intanet yana da matuƙar sauki, maimakon mutum ya tafi wata ƙasa domin yin siyayyar kayayyaki, kawai zai duba shafin shagon intanet ya duba abinda yake sha’awar siya, ya duba yanayin ƙarkon abun da kyaun shi, sannan ya duba farashin in yayi mishi sai ya shiga adaɗin kayan da yake buƙata, sai yasa adireshin da yake buƙata a aiko mishi da kayan da ya siya bayan wasu ‘yan kwanaki, wani abun sha’awa shine zaka iya biyan kuɗi ta bankin ka a take ko kuma ka zaɓi ka biya kuɗin kayan in sun iso gareka.

A nan gida Nijeriya ma akwai shagunan siyayya na intanet da suke kawo kayayyaki masu ƙarko da rahusa, waɗanda zasu iya kawo maka duk abinda ka siya har kofar dakinka, ko wajen aiki ko sana’arka, zaka iya zaɓar biyan kuɗi a take ta hanyar banki ko ka zaɓi biya bayan kayan sun iso gareka, wani abun sha’awa shine zaka iya fasa siyan abu ko da bayan an maka odarshi gidanka ko wajen sana’arka, sannan babu wata matsala da zaka fuskanta a yin hakan, ko da ka biya kuɗi to za’a dawo maka da kuɗinka, muddin abun bai maka ba har canja maka ana iya yi.

Yanzu zamu duba wasu shaguna da suka fi shahara anan gida Nijeriya, waɗanda suka fi kawo kayayyaki da ake yayi a duniya, manyan wayoyin hannu ne, kayan sawa na maza da mata ko man shafawa da turare ne, ko na’urar kwamfuta ce duk dai gasunan akwai su a farashi mai rahusa, kuma mafi yawan kayan suna da inganci sosai.

  1. Jumia: kusan sunfi ko wanne kantin siyayya na intanet shahara a Nijeriya da wasu ƙasashen makwobtan Nijeriya, suna shigo da duk wasu nau’in kaya da ake bukata a cikin ƙasar nan, amma sunfi shahara da shigo da kayan sawa da kuma kayan wuta waɗanda suka hada da wayoyin hannu, nau’rar kwamfuta, talbijan na zamani, da sauransu, wannan kantin na Jumia yana da arahar kaya sosai sannan suna kawo wa mutum odar kayanshi cikin kwanaki biyar a duk birnin da yake a faɗin Nijeriya da wasu ƙasashen makwobta ma, wato litinin zuwa Juma’a sannan kuɗin odar bai taka kara ya karya ba, bayan haka akwai manyan shagunansu da mutum zai iya ziyarta domin karbar kayan da yayi oda. Zaka iya ziyartar shafinsu ta jumia.com.ng
  2. Konga: suma kamar Jumia ne duk da shafin jumia ya ruga shafin konga fara kasuwancin intanet, amma fa suma ba tayar baya bane a harkar kasuwancin intanet, wani abun sha’awa da wannan shafin na konga shine suna da abokan kasuwanci da suke iya daura kayayyaki a shafin konga ta yadda in mutum yana buƙatar wani abu a konga amma basu da shi to sai kawai ya duba a shafin abokan hulɗar konga, sannan akwai bambanci farashi daga shafi zuwa shafi wannan shi zai ba masu sha’awar siyan kayayyaki damar zaɓen shafin da ya fi burgesu.

Zaka iya ziyarta konga ta nan konga.com.ng

  1. Kaymu: su ma dai kamar sauran shagunan, amma dais u sun fi siyarda wayoyin hannu, na’urar kwamfuta da kayan sawa na maza da mata, wani abun sha’awa da wannan shafin na kaymu shine yadda suka samar da damar mu’amala ta kut da kut tsakanin masu siyarwa da masu siya, wato zaka iya neman shawara daga masu siyarwa akan duk nau’in kayan da kake son siya, sannan in kayan da ka siya ɗin yana da wata matsala ba zaka sha wahala ba wajen yin Magana da masu siyarwa.

Ana iya samun shafin ta nan kaymu.com.ng

  1. Slot: Shi ma wani shafi ne da ya shahara da siyarda kayayyaki nau’i nau’i, duk sun fi shahara a wayoyin hannu, na’urar kwamfuta da sauran irin waɗannan kayayyakin wutan, shafin slot suna da alaƙa mai kyau da masu siyan kayayyaki daga garesu, ta yadda kana buƙatar abu to cikin ƙanƙanin lokaci zasu yi kokarin kawo maka abunda kayi oda ba tare da wani ɓata lokaci ba, sannan suna arhar kayayyaki sosai, kudin tuƙuicin odar kayayyakin su ma bashi da wata tsada, daɗin dadawa suna ba wa mutum dama ya gwada abunda ya siya in yana da wata matsala ko naƙasu sai a canja mishi a take ba tare da ya ƙara sisin kobo ba.

Ana iya samunsu a shafin na intanet wato slotlimited.com

Akwai ƙarin wasu shagunan amma tabbas a iya waɗannan shagunan guda huɗu mutum zai iya samun kusan duk abinda yake buƙatar siya a sauran shagunan intanet da ake da su a faɗin duniya, sannan siyan kayayyaki a waɗannan shafukan na cikin gida yafi sauki sosai fiye da siyansu a shagunan ƙasashen waje, akwai matsaloli da ba za ka rasa ba a tattare da shagunan, a ƙaro na gaba in Allah yaso zamu duba matsalolin.

 

Exit mobile version