Connect with us

RAHOTANNI

Shaidan Ya Ingiza Ni Na Yi Wa ‘Yata Fyade.

Published

on

Wani magidanci dan shekara 33, Chibuike Kalu, wanda ake zargi da yiwa ‘Yarshi, ‘yar shekara 14 fyade, ya gayawa jami’an tsaro na ‘yan sanda cewa, shaidan ne ya ingiza shi aikata irin wannan aiki.

“ban san me yafaru dani ba, kawai naji ina matukar jin soyayya da sha’awar ‘yata. Wannan aikin shaidan ne,” jamian tsaro suka fadi hakan acikin maganarshi yayin da suke bincikarshi.
Wanda ake zargin, mazaunin Amodu street, Bariga, Lagos an kama shine a ranar 26 ga Yuni, 2020. Ta hanyar taimakon makobtansa wanda suka mikashi ga jami’an ‘yan sanda dake Bariga don cigaba da bincike.
Yace yana kwanciya da ‘yar tashine yayin da matar tashi(uwar yarinyarshi) bata gida
‘yan sanda sun kuma cewa, suna bincike ne don su tabbatar ko cewa wannan shine na farko da yataba kwanciya da yarinyar.
Mai yada labarai na Jami’an ‘yan sandan lagos Bala Elkana ne ya tabbatar da kama uban yarinyar, yace kuma ba da jumawa ba, zasu kaddamar dashi zuwa ga alkali.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: