Connect with us

KIWON LAFIYA

Shan Kayan Zaki Na Da Illa Ga Lafiyar Jiki -Masana

Published

on

Kwararriya a kan harkar abinci Dakta Bisi Abiola ta bayyana cewar kayayyakin abinci masu zaki ba wai na lemun kwalba na zamani wadanda ake sha ba, kamar yadda wasu mutane suke tsammani ba, irin ha kan kuma yana taka rawa wajen samar da yawan sikari wanda ya wuce misali.

Ta bayyana ha kan ne a wani taron wata wata da aka yi ma sunan Wellness dialogue series, ta bayyana mizanin sikari a cikin lemun kwalba, cewar ba wani mai cutarwa bane, ya ma yi kadan a maganar da ake yi ta ya yi yawa.

Ta kara bayyana cewar yawanci sikarin da ake gani a abincin mutane ya taho ne daga kayayyakin da aka yi a kamfani, kamar cake, sweet, cakuleti, da duk wasu kayayyakin sha da suka  kunshi sikari.

“Sikari yana cikin kashi 100 na lemun sha na fruit juice koda yaushe tana cikin kayayyakin marmari, ba a kara shi sikarin. Kamar dai yadda hukumar lafiya ta duniya take nufi dangane da sikari wanda yake ainihi na halal ne yana cikin lemun juice, a ajin “free sugar” kamar dai yadda ta yi bayani.

Abiola ta kara bayanin cewar yadda ake dari dari da sigari, kamarma an manta da amfanin da yake da shi ne dangane da gudunmawar da fruit juice yake badawa a a lafiyarjiki, kamar dai yadda bincike ya nuna.

Idan kuma aka yi la’akari matsalar da ake samu da hakora ta bayyana cewar akwai, sheda wadda ta nuna yawan shan kayayyakin marmari ko kuma fuit juice, sai dai idan ana nufin, kwalbar robar da ake ba jarirai abinci.

“Idan aka kalli shial’amarin ta  yadda ake da shedar da za a bada, ba wani abin dayake nuna shedar da take danganta rashin amfanin kashi 100 na fruit juice, a kan al’amarin lafiya abin daya hada da nauyin jiki cardiobascular da kuma yiyuwar kamuwa da cutar ciwon sikari ta biya”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: