Kwamandan Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi reshen jihar Kano NDLEA Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana cewa an samu raguwar shan miyagun kwayoyi daga kashi uku zuwa kashi daya bisa dari a jihar.
Abdul ya sanar da hakan ne a ranar Juma’ar da ta gabata a lokacin da kwamitin Fadar shugaban kasa da ke yaki da shan miyagun kwayoyi PACEDA suka kai masa ziyara a a ofishinsa da ke karamar hukumar Fagge cikin jihar ta Kano.
Ya ce an samu raguwar shan miyagun kwayoyin ne a cikin wani rahoto na kwanan baya da aka fitar a jihar Legas sai kuma jihar Ogun,inda ya ce, an samu nasarar ce a cikin ‘yan watannin da suka shige.
A cewarsa, tun lokacin da ya fara aiki sun kaddamar shirin da ake kira a turance ‘Operation Sharar Miyagu’ da nufin magance shan miyagun kayan maye.
Ya kara da cewa, a bisa wannan kokarin da suka yi, sun gano cewar masu samar da magungunna su ne suke rabar da magunguna na jabu kuma suna yin kokarin magance su.
Ya ce sun cafko dilolin sayar da magunguna na jabu a kasuwar Sabongari da ke cikin jihar Kano.
Abdul ya kara da cewa, an samu raguwar yin shaye-shaye saboda umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na magance shaye-shayen miyagun kwayoyi a daukacin fadain kasar nan.
A nasa jawabin shugaban kwamitin Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya sanar da cewa, yaki da shan miyagun kayan maye babban kalubale ne a kasar nan, inda hakan ya sanya shugaban kasa ya bayar da umarnin da zai yaki dabi’ar a daukacin fadin kasar nan ta hanyar kafa kwamitin.Ya ce, nauyin da ke kan kwamitin shi ne gano musabbbanin da ya sanya ake shan miyagun kwayoyi don magance matsalar.
Marwa ya bayyana jin dadinsa a kan cewa, shugaban kasa zai dauki matakan da suka dace don magance dabi’ar baki daya a daukacin fadin kasar nan, inda ya ce, daya daga cikin burinsu shi ne kawo karshen ta’ammali da miyagun kwayoyi.
A cewar sa, a shiye muke mu bayar da shawara hukunta dilolin kayan maye da masu rabar dasu a daukacin fadin kasar nan, inda don a cim ma burin hakan suke neman hadin kan malaman addinai da sarakunan gargajiya.
Marwa ya ce, za a kara gigina cibiyoyin killace masu ta’ammali da kayan maye don koyar dasu sana’oin hannu.
Ya ce, daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a kan yaki da shan kayan maye shi ne yadda hukumar NDLEA take cafke masu ta’ammalin, inda kuma kotuna suke sakinsu.
Ya yi kira da a sake sabunta dokar hukumar yadda za su iya samun sukunin cafko masu yin ta’amammlin da kayan maye a daukacin fadin kasar nan don a hukunta su ba tare da wata tangarda ba.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, kwamitin ya kuma gana da sarakunna gargajiya da malaman addinai da kuma matasa sama da 500 a karamar hukumar.