08148507210 (TES Kawai ) leadershipayau.com
Sallama cikin aminci a gare ku ya ku makaranta wannan jarida ta LEADERSHIP A YAU LAHADI. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah Ya tabbata ga shugaban halitta, Muhammad Dan Abdullah. Bayan haka, Ina mai gabatar mu ku da wannan jarida mai albarka a karon farko, sannan kuma Ina mai gabatar mu ku da wannan shafi mai taken MAHANGA, wanda zai cigaba da fitowa a bangon bayan jaridar nan taku mai albarka.
To, amma ku sani cewa, a matsayina na edita ba ni ne zan rika yin rubutu a wannan shafi ba, har sai dai idan hakan ta kama. Daraktan Editoci da kansa, Malam Musa Muhammad, ne zai rika tattaunawa da ku a wannan shafi. A yau Ina yin sharar fage ne kawai; Ina share wa babban daraktanmu hanya.
LEADERSHIP A YAU LAHADI za ta kasance ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da kare muradun kasa, kwato wa wanda a ka tauye hakkinsa, jajircewa wajen tabbatar da gaskiya tare da fadakarwa da nishadantarwa.
To, wannan shafi na MAHANGA ya na daya daga cikin manyan shafukan da za su taya mu tabbatar da wannan akida da mu ka sanya a gaba. Don haka in sha Allahu wannan shafi na MAHANGA zai rika dauko muhimman batutuwa ya na tattauna su kuma ya na kawo mafita a cikinsa.
Ba wai kawai matsalar za mu tattaunawa a kai ba, illa dai za mu yi kokari mu ga cewa, mun zo wa da dukkan masu ruwa da tsaki, kan duk batun da mu ka dauko, cikakkiyar mafita, domin a taru a fitar da jaki daga cikin duma.
Hakika Nijeriya ta na fama da matsaloli daban-daban, wadanda su ka hada da matsalar tattalin arziki, matsalar tsaro, matsalar ’yan bil adama, matsalar cin hanci da rashawa, matsalar kabilanci, matsalar bangaranci, rikice-rikicen addini, nakasun siyasa da dimukradiyya ita kanda da dai sauran matsaloli da su ka dabaibaye kasar kuma su ke kawo ma ta dabaibayi da tarnaki wajen cigabanta.
Bias la’akari da arzikin da Nijeriya ke da ita, yakamata a ce kawo yanzu irin wadannan matsaloli da mu ka zayyana a sama, an wuce a kasar ta yadda bai kamata a ce har yanzu su ne manyan matsalolinmu ba. Ya fi dacewa a ce, yanzu matsalarmu ita ce ta yadda za mu iya kera abubuwan da wasu kasashen duniya ba su kera sub a.
Wato ya zamana cewa, kamata ya yi na ce gasar cigaban duniya mu ke yi ta hanyar jera wa kafada da kafada da sauran manyan kas ashen duniy. Amma babban abin takaici ne a ce har yanzu mu na maganar ginin hanyoyi, ajijuwa, albashi, ruwan sha, wutar lantarki, magani a aisibiti da sauran abubuwan da tuni duniya ta mance da matsalarsu! Babban abin kunya ne a ce har yanzu akwai kasuwar janareto a Nijeriya. Kasashe masu tasowa ma sun wuce wannnan gurin ballantana Nijeriya ‘UWAR AFRIKA’!
Haka nan kuma ba matsalar shugabanci ko jagoranci kadai za mu rika tattaunawa ba, a’a, hatta matsalarmu ta talakan Nijeriya, ita ma za mu rika tattauna ta a cikin wannan shafi naku, kamar matsalar rashin da’a, keta, hassada, kyashi, munafunci, sana’a, makotaka, dogaro da kai, bara, almajirci, karya doka, maula, tukin ganganci, rashin tarbiyya, shaye-shaye, dabanci da sauran abubuwa na matsaloli wadanda mu talakawa mu ka yi katutu a cikinsu.
Abin nufi a nan shi ne, a cikin wannan shafi za mu rika yiwa junanmu tsumagiyar kan hanya fyade yaro fyade babba!
Lallai wannan aiki na namu ba ne mu kadai. Aiki ne wanda hatta ku masu sauraro ku na da gudunmawar da ya wajaba ku bayar ta hanyar karfafa ma na gwiwa da bayyana ra’ayoyinku a cikin mutuntaka da sanin ya kamata.
Burinmu shi ne mu taimaka wajen ganin rayuwar kasarmu ta inganta, farin ciki ya yawaita kuma kyakkyawar rayauwa ta yalwata. A kokarinmu na cika wannan buri, mun san cewa, ba karamin kalubale ba ne a gabanmu, domin duk wanda ya ke da hannu a cikin irin matsalolin da mu ka zayyana, ta yiwu zai dauke mu a matsayin makiyinsa, alhali ba haka ba ne.
Babban abinda ya kiamata mu gane shi ne, idan kasa ta cigaba kuma rayuawa ta inganta, sannan a ka samu yalwar arziki, to da nagari da mugu duka za su amfana da hakan. Watakila ma daga lokacin sai mugun ya gane cewa, babu sauran amfani a gare shi ci gaba da aikata muguntar, domin watakila a lokacin ba ya cikin fargabar da ta sanya shi aikata muguntar.
Misali a na shi ne, idan arziki ya yalwata, tattalin arziki ya bunkasa, kowa ya wadata, za ka tarar cewa cin hanci da rashawa ya na yin karanci, domin masu yin watakila su na yi ne saboda tsoron talauci. To, ka ga idan talaucin ya yi karanci kuma kowa ya san cewa ya na da kyakkyawar makoma, sai hankali ya kwanta a rage satar dukiyar al’umma.
To, kun ga ashe kenan shi kansa mugun, idan ya tsaya ya yi tunani da ‘MAHANGA’ mai kyau, zai ga cewa, ba kin sa mu ke yi ba, a’a, mu na so ne mu ga cewa, abinda ya ke son ya yi ya aikata shi kuma ya cimma burinsa ta hanya halastacciya. Idan kudi ka ke son samu, to ka samu na halak. Idan ’yanci ka ke nema, ka same shi ta hanyar doka. Wannan shi ne abinda ya dace kuma ya wajaba a dora kasar da ’yan kasar a kai bakidaya.
Hakika wannan babban aiki ne wanda ya shafi kowa. Mu kadai ba za mu iya ba, illa dai kawai za mu yi kokarin ganin mun bayar da tamu gudunmawar, amma tabbas LEADERSHIP A YAU LAHADI, ba za ta iya ita kadai ba. Ku ma sai kun taya mu, domin masu hikima su na cewa, hannu da yawa maganin kazamar miya!
Don haka mu na neman gudunmawar kowa da kowa. Akwai dama cikakkiya ga wanda ya turo da makala mai kyau da inganci, za mu buga ta a wannan shafi da yardarm Allah!
Ina mai tabbatar mu ku da cewa, bias yardarm Allah shi wanda zai kula da wannan shafi, wato Malam Musa, zai yi mu kiu jagoranci nagari cikin amana da ‘MAHANGA’ mai kyau.
A karshe Ina mai yi mu ku fatan alheri tare da rokon ku a kan ku saka ni cikin addu’o’inku a wannan sabon mukami da a ka dora mi ni alhakin kula da wannan jarida taku ta LEADERSHIP A YAU LAHADI. Hadiminku kuma Editanku, Nasir S. Gwangwazo. Bissalam!