CRI Hausa" />

Sharhi:Mai Laya kiyayi mai Zamani

Sakamakon ci gaban da aka samu wajen nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19 a sassa daban daban na duniya, ya nuna cewa, gwagwarmaya da bil Adama ke yi kan cutar zai kawo karshenta.

Amma bayan an gano wani sabon nau’in kwayar cutar a kasar Birtaniya da ma Afirka ta kudu, hankalin jama’a ya sake tashi, har ana tunanin cewa, watakila gwagwarmayar za ta dauki dogon lokaci.
Bayan samun wannan labari, ba tare da bata lokaci ba, gwamnatocin wasu kasashe musamman ma na Turai su ka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa da na sama a tsakaninsu da Birtaniya, baya ga sanar da sabbin matakan binciken lafiya da ma rufe kan iyakokin kasashensu. Da alama, annobar mai ban tsoro ta sake fara yaduwa ba zato ba tsammani.
Idan har ana son tinkarar wannan sabuwar matsala, da farko dai, bai kamata kasashen duniya su ji tsoro ba. A maimakon hakan, ya kamata a yi amfani da ilmin kimiyya da sanin ya kamata don kau da rashin tunani.
Abin farin ciki shi ne, wani jami’in hukumar kiwon lafiyar duniya WHO ya bayyana cewa, bisa labarin da suka samu, an ce, kawo yanzu ma dai, babu shaidu dake nuna cewa, sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 zai rage tasirin allurar rigakafin da wasu kasashen duniya suka samar.
Wani muhimmin darasin da bil Adam ya koya a cikin ’yan watannin da suka gabata, shi ne muddin kasa da kasa sun dauki kwararan matakai yadda ya kamata, to tabbas za a iya samun nasara a kan cutar duk wayon ta.
Wani albishiri shi ne, duk da yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 da wadanda suka mutu sakamakon cutar na cigaba da karuwa, amma yanzu duniya ta samu kwarewa wajen yaki da cutar in an kwatanta da na baya, ganin yadda ba a san komai ba kan cutar a wancan lokaci.
Yanzu ana kokarin kafa shingen kare bil Adama daga cutar, ganin yadda shirin samar da allurar riga kafin cutar ke ci gaba a duk fadin duniya, kana ake gwaji da ma amincewa da alluran rigakafin daban daban, Ko da yake akwai sauran rina a kaba.
Bullar sabon nau’in kwayar cutar COVID-19 ta sake aikewa da wani gargadin cewa, dole ne dan Adam ya kasance cikin shirin yaki da cutar cikin dogon lokaci, sannan kada gwiwar kasashen duniya ta yi sanyi. Muddin kasashen duniya suka hada kansu wajen yaki da cutar, a kokarin raya makomar bil Adama ta bai daya ta fuskar kiwon lafiya, tabbas, wata rana, za a kawo karshen cutar har ta zama tarihi. (Kande Gao)

Exit mobile version